An sace kayan masarufin ‘Yan gudun hijra a Adamawa

An sace kayan masarufin ‘Yan gudun hijra a Adamawa

–An nemi kayan abincin ‘yan gudun hijira an rasa a Jihar Adamawa.

–Hakiman unguwannin na kira ga gwamnatin tarayya tayi bincike akan akan al’amarin

–Wata bincike ta nuna ba yau aka fara aikata wannan abin kunya ba.

Bacewan tireloli 71 cike da Shinkafa da wasu kayan abincin da gwamnatin tarayya ta baiwa ‘yan gudun hijran jihar adamawa ya kawo tashin hankali a yankin. An bada rahoton cewa gwamnatin tarayya ta turo agajin tireloli 71 cike da kayan masarufi ga ‘yan gudun hijira ,wanda mataimakin gwamnan Jihar Adamawa, Mr. Martins Babale ya kaddamar.

An sace kayan masarufin ‘Yan gudun hijra a Adamawa
yan gudun hijira

Jaridar Guardian ta bada rahoton cewa har yanzu kayan abincin bai iso wajen ‘yan gudun hijiran ba,aka samu labarin bacewan  su. Mr. Emmanuel Tsamadu, wanda mamban majalisar dokokin Jihar Adamawa ne ,ya ce shugabannin unguwanni sun bayyana cewan buhuhunan shinkafa 250 kawai ya iso wurinsu sabanin buhuhuna 1200. Ya na kira ga gwamnatin tarayya da ta gudanar da binciken wannan satan abincin yan gudun hijiran da ke halin kakanikaye.

Hakimin garin Gulak hedkwatan madagali, Mr. Bello Ichadi, ya bayyana cewan hakimai 5 kacal suka samu rabin buhun shinkafa 50, wanda ya ke jimillan rabin buhun shinkafa 250 ga garin Madagali gaba daya. Wanda duk da cewan su suka fi azabta da rikicin Boko Haram saboda kusancin ta da dajin sambisa.

KU KARANTA : Dan Boko Haram ya kashe kansa a Masallacin Juma’a

Daga baya aka gano cewan rabin buhun shinkafa aka kawo a maimakon buhu cikakke. Mr. Haruna Furo,wanda shine sakataren hukumar kawo agaji ta gaggawa watau ‘State Emergency Management Agency’ yace duk da cewan ma’aikatar su ke da hakkin kula da ‘yan gudun hijiran, bata da hakkin raba abincin da gwamnatin tarayya ta bayar. Ya ce: “Gaskiya ban san abinda ya faru da rabon abincin ba, duk da cewan hukumar mu ke da hakkin kula da yan gudun hijira. amma ba da mu akayi shirin rabon ba, anyi ne a Abuja. Mutane basu gushe suna kiran ofishi na ba suna kawo kuka, amma gaskiyar Magana it ace bamu san yadda akayi rabon ba,ba da mu akayi ba.

Amma,wani binciken da Gidan Jaridar Legit.ng  ta gudanar ya bayyana cewan wasu yan tsirarai ne da ke cikin hukumar kawo agaji ta gaggawa na tarayya watau ‘ National Emergency Management Agency’ ne suka sace abincin ‘yan gudun hijiran. Wata majiyar mu ta bayyana cewan ‘yan tsirarun sun dade suna irin wannan babakeren da dadewa,a maimakon ciyar da mabukata,’yan gudun hijra.

 

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng