Taba ka lashe: Yadda ake gane kwai maras kyau cikin sauki!

Taba ka lashe: Yadda ake gane kwai maras kyau cikin sauki!

Kwai dai wani abin ci ne mai cike da sinadaran da ke kara lafiya kuma yana da saurin dahuwa kar harma da dandano mai dadi. Sai dai kash kuma kwai yana da saurin lalacewa.

Yi tunanin misali ace ka/kin shirya tsaf don yin karin kumallo kuma ki/ka na son cin kwai kawai sai ka fasa kaga ya lalace kuma yana wani irin wani maras dadi, Wata kila hakan ta taba faruwa da kai/ke ko?

Taba ka lashe: Yadda ake gane kwai maras kyau cikin sauki!
Taba ka lashe: Yadda ake gane kwai maras kyau cikin sauki!
Asali: UGC

KU KARANTA: Jirgi mai saukar angulu na sojin Najeriya yayi hatsari

To ku sha kurumin ku, ga wata hanya nan da za'a iya gane kwai maras kyau da mai kyau cikin sauki.

*Zuba ruwa cikin wani dan kofi ko kwano sai ka saka kwan da kake so ka auna ka gani. Idan ya nutse ciki duka do yana da kyau. Idan ma sai da ya dan tsaya saman ruwan sannan ya nutse, to shima yana da kyau za'a iya ci amma a sani cewa ya kusa lalacewa shi. Amma idan kana sa shi a ruwan kaga ya taso a sama to tabbas wannan ya lalace.

Ga wasu karin dabarun anfani da kwai din kuma:

*Idan ana so a ajiye kwai ya dan dade to kar a sa shi cikin firjin don kuwa ciki sanyi gare shi kuma hakan zai sa ya lalace. A maimakon haka sai a ajeshi a waje amma kuma cikin inuwa da ni'ima.

*Bayan kwai yana daukar kwayoyin cuta da yawa don haka kafin a ajiye kwai a wurin dake akwai abinci, ya kamata a wanke bayan da ruwa masu kyau sosai.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng