Griezman ya kai Faransa ga wasan karshe a gasar EURO 2016
Ya tabbata Faransa zata hadu da kasar Portugal a wasan karshe na gasar EURO 2016. Masu masukin baki Faransa ta lallasa Jamani ci 2 da babu-0 ta hannun dan was anta Griezman. France dai it ace ta mamaye wasan in da ta samu bugun daga kai sai gola a gab da tafiya hutun rabin lokaci a yayin da shugaban yan wasan Jamani Schweinsteiger ya kama kwallo da hannu a cikin gidansu, inda shi kuma Griezmann bai yi wata wata ba ya zura kwallo a raga bayan ya siyar da golan Jamani Manuel nuer, a haka dai aka tafi hutun lokaci france na jograntar wasan 1-0.
Kasar Faransa ta dawo daga hutun rabin lokaci da kwarin gwiwa sosai inda ta ci gaba da murza leda. Ana nan sai dan wasan tsakiya na Faransa yayi wani juyin da ya kawo wata kwallo, amma sai golan Jamani yayi wasa ta kufce mai inda ya tura ta ga Griezmann wanda ya zura ta cikin zare. A haka aka tashe 2-0, Fransa 2, Jamani 0. A yanzu dai Faransa zata fuskanci Portugal wadda ta kori kasar Wales a wasan kusa da na karshe. Za’ayi wasan karshen ne ranar lahadi, 10 ga watab Yulio a kasar Paris.
Ga dai yadda ta kasance a fafatawar.
90+4: Peep Peep! Wasa ya kare bayan alkalin wasa ya hura usur. An tashi ci 2 da babu Faransa ta ci Jamani
90+3: Golan Faransa Lloris ya tare wata kwallo daga shiga raga da kyar
90+1: an cire Griezman, an sako Cabaye
90: an kara mintuna 4
88: Faransa ta rike wasan yadda take so
85: Ana cin Jamani kwallo 2, ba’a taba zaton irin sakamon kon nan ba. Faransa na taka leda yadda ya kamata
82: dan wasn Jamani Howedes ya sa ma wata kwallo kai, sai dai tayi yawa.
79: Jamani ta yi canji an cire Schweinsteiger, Sane ya shigo
77: dan wasan Jamani Draxler ya doka wata kwallon da ta fita, Fransa sun cire Giroud, Gignac ta shigo
75: wasan tayi wa Faransa kyau, sun rage ma wasan zafi. Ya rage sura mintin 15 a tashi
73: GOOOOOOAAAAAAAAAAALLLLLL!!!! Griezmann ya zura kwallo ta biyu a zaren Jamani. Pogba ne ya kawo wata kwallo, sai Gola Neur yayi sakaci ta fado ma Griezmann.
71: Payet ya fita, France ta canje shi da N’Golo Kante
70: Mustafi yasa ma wata kwallo kai, sai dai tayi yawa
67: Dmitry Payet ya samu daman zura kwallo, sai dai bai doka kwallon da kyau ba
65: Pyet ya fadi a kasa, a sha shi da kwallo. Faransa ba zata so wani abu ya samu dan wasan tab a wannan lokaci
63: Koscielny ya sa ma wata kwallo kai, sai dai tayi yawa
61: Mustafi ya canji Boateng dan kasar Jamani da ya samu rauni
60: Jerome boating ya fadi kasa warwars, likitoci na duba lafiyarsa
57: An kwaso ma Hector kwallo mai kyau, sai dai ya kasa rike ta. Faransa ta samu bugun gida
55: Koscielny ya tsare gida da kyau, sai dai alkalin wasa ya hango cuta, a ya baiwa Faransa bugun tazara
52: Evra ya nuna tirjiya da kyau don hana draxler buga kwallo.
50: Draxler ya samu katin gargadi bayan ya yi Sissoko mugunta
48: Faransa suna yunwa kara cin wani kwallon, sun san Jamani na da hatsari
46: Olivier Giroud ya barar da wata kwallo daga dawowa daga hutun rabin lokaci
HT: An tafi hutun rabin lokaci
45+1: GOOOOOOOAAAAAAAAALLLLLL! Antoinne Griezmann yaci bugun da kai sai gola. Faransa ta shiga gaba
45: Faransa ta samu bugun da ga kai sai gola. Shugaban yan wasan Jamani Schweinsteiger ya samu katin gargadi
45: Faransa ta dage tana take leda.
42: Giroud yayi ragwanci, wata kwallo ta zo mai a sadaka, kuma yana kallon raga, amma yayi sanyi har Howedes ya za da zafinshi ya dauke kwallo
40: Pogba ya kai Schweisteiger kasa a cikin gidan su, amma alkalin wasa yace ba laifi
37: Pogba ya buga bugun tazara mai kyau har raga, amma gola Neur ya kama kwallon
35: Faransa ta samu bugun tazara a kusa da gidan Jamani, Emre-Can ya samu katin gargadi
32: Jamani ya buga wasa yadda take so, suna buga wasa a cikin gidansu
28: Griezmann ya ja masu tsraon faransa da gudu, sai dai sakin kwallon yayi yawa, Payet bai sa me tab a.
26: Schweinsteiger ya doka kwallo hammatan raga, sai dai Lloris ya tare ta.
24: Payet ya buga bugun tazara, Nuer ya tare.
20: Toni kroos ya kwaso kwallo mai kyau cikin gidan Faransa, amma Koscielny ya cira ta.
16: Hector ya yi wa Pogba dabara ya kwace kwallo.
14: Gola Lloris ya tare wata kwallo da Emre-Can ya buga, ya hana shi cin kwallo
12: Yan wasan Jamani sun samu nutuswa a cikin wasan, sai dai Emre-Can ya barar da wasa
9: Jamani masu rike da kambun Gasar, na kokarin rike kwallon
6: Griezman da Pogba sun yi rawar gani, sai dai Nuer ya tare bugun da yayi wa kwallon.
4:Yna Jamani na fama da Faransa, saboda yawam magoya bayan su
2: Faransa ta samu bugun kwana da na farko.
1: an fara wasa, cikin su wanene zai hadu da Portugal a wasan karshe?
Ga jerin yan wasan
Jamani: Neur, Hector, Howedes, Schweisteiger, Ozil, Draxler, Muller, Can, Boateng, Kroos, Kimmich.
Faransa: Lloris, Evra, Umititi, Koscielny, Sagna, Matuidi, Pogba, Payet, Griezmann, Sissoko, Giroud.
Wasan Faransa maus masaukin baki da Jamani masyu rike da kambu a wasa na 2 na gasar cin kofin nahiyar turai na 2016
Faransa bata tab cin Jamani ba a kowanne irin wasan tun 1958, kuma gwarzon wannan wasa shine zai hadu da Portugal a wasan karshe tun bayan cire Wales da tayi. Masu masukin bako sun lallasa kasra Iceland kwallo 5 da 2 ranar Lahadi sa’annan suka hauro zagaye na uku.
Sai dai dole a yanzu yaran Didier Deschamps su nemo hanyar doke masu rike da kambu-Jamani, dukkanin su ana zaton zsu iya cin kofin, duk da cewa shekaru aru aru rabon da Faransa ta ci Jamani.
Kocin Jamani Joachim Lowa ya bayyanar da cewa dan wasan tsakiyan Manchester Bastian Schweisteiger ne zai jagoranci ya wasan sa bayan dawowar sa daga jinya. Sai dai Hummels ba zai yi Jamani wasa ba, tunda an sallame shi daga gasar, shi kima Mario Gomeza Sami Khedira sun samu raunuka. Ya samu raunin ne a hannun sa. Faransa kuwa basu da matsalar raunuka, asali ma suna murnan dawowar Adil da N’Golo kante daga sallamar da aka musu a wasan da suka lallasa Iceland 5-2.
Suko yan wasan Arsenal Olivier Giroud da kuma Laurent Koscielny an cire su a wasan Iceland don kada su samu raunuka. Wannan shine haduwa na biyar tsakanin Jamani da Faransa. Farsansa sun lashe haduwa ta farko 6-3 a gasar cin kofin duniya ta 1958.
Asali: Legit.ng