Kannywood ta yi rashin Cinnaka

Kannywood ta yi rashin Cinnaka

-Yau 8 ga watan Yuli ne ake sadakar uku na rasuwar Baffa Cinnaka dan wasan barkwancin a fina-finan Hausa 

- Baffa Ahmed wanda aka fi sani da Cinnaka na daya daga na hannun daman Ibro

-Ciwon ciki ne ajalin marigayin  

Kannywood ta yi rashin Cinnaka
Marigayi Baffa Cinnaka da Auwalu BB Hotoro da kuma Rabiu Daushe

Masana’atar shirya fina-finan Hausa da aka fi sani da Kannywood ta za ta dade ta na jimamin rashin Baffa Ahmed wanda aka san da Cinnaka, daya daga cikin ‘yan wasan barkwanci da ya yi suna a wasan ban dariya.

A cewar Auwalu BB Hotoro, daya daga cikin abokan marigayin da suke yin wasa tare, “Baffa Cinnaka mutum ne mai zumunci da kyautatawa ‘yan uwa kuma ba shi da abokin fada”. Baffa  Cinnaka na daya daga cikin na hannun daman marigayi Rabbilu Musa dan Ibro  a fina-finan barkwanci da aka fi sani da Camama.

Kannywood ta yi rashin Cinnaka
Baffa Cinnaka (hugu) da Baba Ari (dama)

shi ma a shafin sa na Facebook Baba Ari, wanda ya bayyana Baffa a matsayin abokinsa na kut-da-kut, ya ce za'a dade ba'a manta da marigayin ba, ganin irin rawar da ya ke takawa a wasan ban dariya a fina-finan Hausa.

Dan shekara 42 da haihuwa Baffa Cinnaka ya rasu ne a gidansa da ke Wudil a safiya ranar Litinin 5 ga watan Yuli. Bayan ya kamu da ciwon ciki bayan gama cin abincin sahur na asubahin ranar Litinin a lokacin da ake shirin daukar azumin wannan rana. An kuma garzaya da shi Asibiti a inda rai ya halinsa.

Marigayin ya mutu ya bar matar daya da ‘ya ‘ya 6, ya kuma rasu ne kwanaki 6 da rasuwar yayansa wanda ya ke bi a haihuwa, an kuma daga sadakar uku na rasuwar zuwa ranar bakwai kamar yadda wani makusancin marigayin ya bayyanawa Legit.ng.  Shiri na karshe da marigayin ya yi shi ne a wani fim mai suna Hedimasta  a inda ya fito a matsayin shugaban makaranta.

 

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng