Torres zai cigaba da zama Atletico Madrid   

Torres zai cigaba da zama Atletico Madrid  

Shahararren dan kwallon kasar Spain Fernando Torres ya kara rattaba hannu a kan wata kwataragin da zata sa ya cigaba da zama a kulob din sa na Atletico Madrid biyo bayan cikar wa'adin zaman sa AC Milan.

Torres zai cigaba da zama Atletico Madrid   

An bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da kulob din ya fitar ta tashin yanar gizon sa. An dai ruwaito cewa Torres din ya fada ma kulob din nasa na Atletico cewar: "Na ji dadi zan cigaba da buga kwallo ta a gida. Kamar kowane dan wasa dai, nima ina son in cigaba da zama a gida ina buga kwallo ta".

"Ina jin dadin zama na a nan. Ban taba kokwanton hakan ba. Duk tsawon lokacin nan da na shafe ina buga wasa a nan ina ta mafarkin zama cikakken dan kwallon nan kungiyar ne daman." Shi dai dan wasan ya rattaba hannu ne a biya wata yarjejeniya da zata sa ya ci gaba da zama kulob din.

A nashi bangaren, shugaban kungiyar ta Atletico Jose Luis Caminero cewa yayi kulob din nasa yana matukar farin ciki da faruwar hakan. Yace tabbas dan kwallon zai zama abun koyi ga wurin da yawa daga yaran kulob din masu tasowa.

Yace: "Wannan wani labari ne mai dadi ga kowa. Dan wasan ya zama kamar dan uwa ne ma ka shugabanni tare da magoya bayan kulob din don haka kowa najin dadi ganin zai cigaba da kasacewa tare da mu. Ya san kulob din ciki-da-bai don haka kowa na son sa.

"Tawagar kungiyar ma na yara masu tasowa suna son sa sosai don ya zama abin koyi kare su da kuma bada shawarwari." Shi dai Torres din ya je Atletico ne a matsayin dan aro har na watanni 18 daga AC Milan a watan Janairu na 2015. Kuma dama a nan kulob din ya fara buga wasan kwallo tun yana shekara 17 a 2001.

Asali: Legit.ng

Online view pixel