Zuwan Mourinho yasa Ryan Giggs Barin Manchester
-Ryan Giggs ya bar kungiyar saboda hanashi zama mataimakin mai horarwa
-Jose Mourinho yana da niyyar bada matsayin na mataimakin ga dadadden abokinshi Rui Faria.
-Dan wasan kwallon kafa mai tarihi a kungiyar manchester united ya kawo karshen zamanshi na shekara 29 da kungiyar saboda zuwan sabon kocin Jose Mourinho.

Ana tsammanin Kungiyar zata saki sanarwar tafiyarshi nan da kwanaki masu zuwa duk da rade-raden da mutane keyi na barin dan wasan na gefe a kungiyar. Dan shekara 42,yana da sauran shekara 1 a kwantaraginshi na matsain mataimakin mai horarwa,amma sabon kocin ya nuna ra'ayinshi na nada dadadden abokinshi a matsayin mataimakin.
Saboda kasa gama yarjejeniya a kan bashi wani matsayi,Giggs ya yanke shawarar baarin kungiyar da yake tun yana dan shekara 14. Giggs ya kafa tarihin buga wasa a kungiyar har 963,sa'an nan beta ba boye ra'ayinshi ba na kutsawa cikin rukunin masu horarwa,Giggs ya bar kungiyar da bacin rai da jin yana shirye da ya hori kungiyar.
KU KARANTA : Chelsea ta sayi Michy Batshuay daga Marseille
Dan wasan be ji dadin yadda Luis vangaal ya bar kungiyar,lokain da labarin sallamar mai horar ya zomai bayan yayi nasarar lashe kofin FA Cup,Giggs be ji dadin abinda masu zartar da hukunci a kungiyar suka yi ba na tsallakeshi da akayi a ka ba tsohon mai horar da kungiyar na chelsea da Real madrid wato Jose Mourinho.
Tsohon dan wasan wales yaci kofuna premier 13,Champion league 2,FA cup 4 da kuma carling cup wanda yasa ya zama kayataccen dan wasa a nahiyar Turai.
Asali: Legit.ng