Arsenal Ta Tabbatar Da Sayen Dan Kwallon Kasar Japan.
-Tukuma Asano ze tafi Arsenal wannan shekarar daga Kungiyar kwallon Sanfreece Hiroshima.
-Arsenal ta tabbatar da doke manyan kungiyoyi gurin sayen Tukuma.
Arsenal sun kai karshen yarjejeniyar da sukayi na sayen matashin dan wasan gaba na kasar Japan Tukua Asano daga kungiyar Sanfreece Hiroshima.
Dan shekara 21 na kasar Japan ze zama dan wasan Arsenal bayan kammala gwaje-gwajen lafiya da sauran abubuwan da ya kamata.Kungiyar ta arsenal ta fada cewa"Manyan kungiyoyi sun nemi sayen Tukuma. Arsene Wenger yace"Tukuma yaro ne mai buga kwallon gaba mai hazaka kuma zeyi kokari nan gaba.Yana da kayataccen fara taka leda a kasar Japan,kuma muna tsammanin cigabanshi a shekaru masu zuwa.
Dan kwallon na gaba ya fara buga ma kasar japan wasa a watan August 2015,a halin yanzu ya buga ma kasar tashi sau 5 kuma a na tsammanin ze kasance 1 daga cikin wadanda zasu buga ma kasar ta japan kwallo a gasar Rio olympic a watan August.Tukuma ya tafi kungiyar Sanfreece Hoshima yana dan shekara 18 watan january 2013,kuma ya samu nasarori a gasar J-league inda ya taka leda sau 56 yaci kwallo 11.
KU KARANTA : Arsenal Ta Tabbatar Da Sayen Dan Kwallon Gaba Na Kasar Japan
A lokacin da yake kungiyar, Tukuma yai gasar J-league a shekara 2013 da 2015,yai japanese super cup 2013,2014 da 2015,sannan a ka zabeshi a matsayin Rookie of the year 2015 a gasa J-league.
Asali: Legit.ng