Mata da yara 772 ‘yan Boko Haram ke tsare

Mata da yara 772 ‘yan Boko Haram ke tsare

-Kimanin mata da yara ‘yan Boko Haram ne 772 ne tsare a Maiduguri

-Mai shari’a Alkali Wakkil ya je ziyarar gani da ido

-Ana faragar ‘yan kungiyar na iya kai hari

Mata da yara 772 ‘yan Boko Haram ke tsare

Mazauna gari Maiduguri na zaman dar-dar a sakamakon yawan mata da yaran ‘yan Boko Haram din da ake tasre da su a wani babban gidan yari a babban birnin jihar Borno. A cewar jaridar Daily Trust kimanin ‘yan Boko Haram yara da mata 772 ake tsare da su domin canza musu tunani, kari ga wasu kimanin 1,288 wadanda ke jiran shari’a ake tsare da su a gidan yarin.

KU KARANTA : Boko Haram tayi gagarumar Asara

Wannan bayani ya fito na a lokacin da mai Shari’a Alkali Gana Wakkil tare da wasu manyan jami’an gwamnati suka kai ziyara a gidan yari daya tilo da ke aiki a jihar, a ranar Litimin da ta gabata.

Mataimakin shugaban kula da gidajen yari na jihar, Lumson Apollos Kaye wanda ya kewaya da jami’an bangaren mata a gidan yarin, ya nuna musu wasu daga cikin mata da yaran da ake tsare da su, suna cikin koshin lafiya, kadan daga cikin iyalan ‘yan ta’addan ne a cerwarsa.

Mista kaye ya koka da rashin samun wani agaji daga gwamnati, a inda ya ce ta kai har kudi suke tarawa daga aljihunsu domin sayen sabulun wanki ga wadanda ake tsare da su. Mazauna Maiduguri dai na cikin zaman dar-dar dangane da yiwuwar ‘yan Boko Haram din su iya kai hari kan gidan yarin, kamar yadda suka yi a Bama da Dikwa a inda aka kona gidan yarin wasu kuma darurruwan firsinoni suka tsere.           

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng