Zuwan Mourinho ya tilastawa Ryan Giggs barin ManUtd
Shahararren dan wasan Manchester Utd mai dadden tarihi Ryan Giggs ya kawo karshen zaman sa a kungiyar tasa bayan ya shafe shekaru 29 da su. Wannan dai ya biyo bayan zuwan sabon mai horaswar kulob din Jose Mourinho.
A jiya asabar ne dai kungiyar ta fitar da sanarwa tafiyar tsohon dan wasan gefe mai dadden tarihin. Giggs wanda kuma shekarun sa 42 yana da sauran shekara 1 cikin kwantaragin sa na mataimakin mai horas wa amma saidai Mourinho baya da ra'ayin yin aiki tare da shi -inda shi Mourinhon ya ke ci gaba da aiki da abokin sa na tun tuni Rui Faria.
Bayan kasa cimma tsayayyar yarjejeniya da kulob din nasa, Giggs ya amince da ya bar kulob din da ya taso cikin sa tun yana shekaru 14 kacal a duniya. Shidai Giggs din ya buga ma kulob din Manchester wasa har sau 963.
Rahotanni dai sun nuna cewa Giggs din bai ji dadin yadda kulob din na sa ya kori Van Gaal ba kuma a bayan korar tasa ma sai suka fifita Mourinho akan sa. Tsohon dan wasan wanda kuma dan kasar Wales ne ya lashe kofuka 13 na firimiya, kofuka 2 na zakarun turai, kofuka 4 na FA da kuma kofuka 4 na Lig' wanda kuma hakan ya bashi matsayin dan kasar Birtaniya wanda ya fi kowa samun kyautuka.
Daga baya ne kuma aka nada shi mataimakin mai horar wa na Van Gaal a shekara ta 2014. Ana dai kyautata zaton Ryan Giggs shine musababbin dauko dan wasan gaban nan na kulob din mai shekara 18 Marcus Rashford.
Asali: Legit.ng