Ga matashin da ya rasa aikinsa saboda Boko Haram
- Sunan matashin wanda ya rasa komai ne Mu'azu Alhaji
- Misiya dan Arewa kuma ne:
Legit.ng ta kawo hakan daga shafin Facebook din na matashin mai kokari. Mu'azu Alhaji Misiya matashi ne wanda ya salwantar da rayuwarsa da aikin sa dan ba da tsaro da zaman lafiya a garin Maiduguri. Mu'azu yana da mata biyu ta yara shida.
KU KARANTA KUMA: Yan Neja Delta sun gargadi Buhari game da Maritime
Mu'azu wanda mazaunin garin Bama ne, ya yi aiki a wani bankin first Bank dake garin Maiduguri, amma daga bisani ya ajiye aikinsa saboda ya samu damar yakar 'yan Boko Haram. Mu'azu ya kasance mutum mai muhimmanci a farautar da dakarun sojoji ke fita da su a matsayin 'yan bangan sa kai inda yana matukar taka muhimmiyar rawa a nasarar da sojojin suke samu kan 'yan Boko Haram. Ana zaton Mu'azu yana da asirin rashin tashin bindiga, wanda hakan ya sa sau da yawa idan sun yi gaba da gaba da 'yan Boko Haram bindigar su ba ta tashi. Sannan kuma an shi yunkurin kashe shi amma Allah bai nufa ba.
Al'ummar garin Bama da Maiduguri suna yi wa Mu'azu kallon jarumi, sakamakon muhimmiyar rawar da ya taka wajen rage karfin 'yan Boko Haram a jihar Borno. Kuma hakan ya sa sojoji suna son fita farauta jeji da shi domin yakan taimaka musu wajen samun nasara. Saidai duk da wannan gudummawa da Mu'azu ya bayar, bincike ya nuna cewa babu wani tallafi da ya samu kama daga gwamnatin tarayya da ta jiharsa ta Borno, duk da cewa ya jima da rasa aikin bankin da yake yi sakamakon sadaukar da rayuwarsa da ya yi domin yakar 'yan ta'addan da suka addabi jiharsa.
Mu'azu ya kasance ba ya samun albashi ko tallafi daga kowane bangare na hukumar tsaro duk da cewa ya bar matarsa da yaransa shida a garin Maiduguri ya dawo Bama da zama saboda yakar Boko Haram. Wasu farautun da aka fita da Mu'azu tun shekaru biyar da ya soma aikin bangar zuwa yanzu sun hada da; Sune Civilian JTF na farko a Maiduguri, Fadan Smbisa, Karbo garin Bama, karbo Gidan Sarkin Bama, Kamo 'yan Boko Haram daga garuruwa da dama. Wanda hakan ya sa sojojin kasa na alfahri da shi.
Saidai abin tambaya a nan shine ko gwamnatin jihar Borno karkashin Kashim Shettima da ta shugaba Buhari ta san da zaman wanna bawan Allah wanda ya sadaukar da rayuwarsa don samar da tsaro a kasar nan? Yanzu haka dai ba ya samun albashi ko gudummawa daga kowane bangare na gwamnati duk da cewa ya jima da rasa aikinsa kuma yana da iyalai. Babban dalilin rasa aikin Mu'azu shine domin wata farauta ta neman 'yan Boko Haram da za a yi da hadin gwiwar sojoji wanda hakan ya bada rayuwar sa ya ajiye aikin sa dan kawo zaman lafiya a kasa da kare al'umma. Amma gwamnatin tarayya da ta jihar Borno ba su san da jarumtar da wannan bawan Allah ya yi ba ta hanyan salwantar da rayuwar sa da aikin sa.
Ku duba hotunan a kasa:
Asali: Legit.ng