Matsalar da Cin hanci da rashawa zasu jawo ma Najeriya

Matsalar da Cin hanci da rashawa zasu jawo ma Najeriya

-Rohoton BMI wanda ke auna hadarin yin kasuwanci a kasashe ya bayyana Najeriya a matsayin daya daga cikin kasashen da ke da hadari wajen yin kasuwanci.

-An gano cewa cin hanci da rashawa ne kan gaba wajen kawo cikas ga harkar kasuwanci.

-An yaba ma shugaba Buhari kan kokarinsa na kauda cin hanci da rashawa.

Matsalar da Cin hanci da rashawa zasu jawo ma Najeriya

An sanya Najeriya a cikin kasashen da ke da wahalar yin kasuwanci a cewar  rohoton BMI na ma'aunin kasashe masu saukin yin kasuwanci na watan Yuli. Kara tabarbarewar sha'anin tsaro, hare-haren 'yan ta'adda da tsananin karancin mai na wasu daga cikin abubuwan da suka taru suka maida kasar mai hadarin yin kasuwanci a Afrika kudu da Sahara. A cewar rohoton "Najeriya na zama kasar da masu zuba jari ke fuskantar hadari da kuma matsanancin yanayin yin kasuwanci a cikin rukunin kasashen da ke kudu da Sahara.

KU KARANTA : Buhari ya karbi bakoncin mambobin sojojin diflomasiyya

Abu mafi hadari ga kasuwanci shine tabarbarewar tsaro wanda 'yan ta'dda da tsagerun masu laifi ke kawowa tare da matsanancin karancin mai da ake fama da shi

Asali: Legit.ng

Online view pixel