Boko Haram tayi gagarumar Asara

Boko Haram tayi gagarumar Asara

Rundunar Soji ta kai wa yan ta’addan Boko haram hari a yayin da suke tserewa daga filin daga. Jami’an tsaro sun hallaka yan Bokoharam a wani hari da suka kai musu a mafakar su yayin da suke tserewa daga filin daga. Sojoji shidda da Yan’sakai na Sibilyan JTF guda biyu ne suka jikkata a yayin fafatawar da suka yi da Yan’tada kayar bayan, kuma an garzaya dasu zuwa Asibiti don samun kyakkyawan kulawa.

Boko Haram tayi gagarumar Asara

Wasu daga cikin makaman da aka kwato daga Yan ta’addan sun hada da Babura, Bindigu iri iri, Bama bamai da dai sauransu. Wannan yana daya daga cikin koma baya da yan kungiyar Boko haram suke fuskanta tun banayn hare haren da rundunar Sojan Kasar nan ta fara kai musu a yayin da suke neman hanyoyin tserewa daga fushin hadakar Sojojin Kasashen dake makwabtaka da Najeriya. Yan ta’addan sun harbi wata motar yaki ta musamman mallakan Sojoji, inda tankin mai da wasu wayoyin wutar Motan sun lalace.

Wata sanarwa daga bakin mukaddashin daraktan mu’amala da mutane na hukumar Soja Kanal Sani Usamn Kuka-sheka ta ce sun hallaka yan ta’adda da dama a harin da suka kai musu a mafakarsu da ke Kangarwa a yammacin jiya 29 ga watan Yuni, kuma da yawansu sun samu sha raunuka irin na harbin bindiga.

Usman ya kara da cewa Sojoji 8 da Sibilyan JTF 2 sun samu raunuka, amma an dauke daga filin daga daon samun kulawar data dace, cikin ikon Allah suna samun sauki. Kakakin ka kara da cewa a yayin gumurzun, an har ba gurneti akan wata motar yakin soja kuma hart a kama da wuta, amma Sojoji sun kashen wutan da gaggawa.

Kamar yadda Usman ya fadi, wasu dag cikin kayayyakin da aka kwato daga yan ta’addan su hada da Babura, Bindigu iri iri, Bama bamai, cajojin waya, alburusai, tayar mota da kuma kwayoyi. Ga hotunan kadan daga cikin su.

Boko Haram tayi gagarumar Asara
Boko Haram tayi gagarumar Asara

A wani ci gaban, Shugaban Kasa Muhamadu Buhari yace Gwamnatin sa zata sake gina yankin Neja Delta. Hakam ma kunshe ne a cikin wata takardar da aka raba ma manema labarai ta hannun mataimaki na musamman ga Shugaban Kasa akan harkokin yada labarai Mista Femi Adesina a ranar Alhamis 30 ga watan Yuni. A cewar  Adesina, Shugaba Buhari na bukatar juriya da fahimmata daga Yan Najeriya don cimma wannan manufa. Buhari yayi alakawarin ne a lokacin da ya karbi bakwancin wakilan tattaunawa da sulhuntawa na Neja Delta karkashin jagorancin Mai martaba sarkin garin Brass Alfred Ditte-Spiff a fadar sa dake Abuja, inda ya bada tabbacin Gwamnatin sa zata tattala arzikin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel