Manchester  zasu siya Neymar, zamu siyar- Barcelona

Manchester zasu siya Neymar, zamu siyar- Barcelona

Da alamar shahararren dan kwallon kasar Brazil kuma mai buga sana’ar kwallonsa a kungiyar kwallon kafa ta Barcelona Neymar zai yi adabo da kungiyar, inda a yanzu haka kungiyar ta fara neman wanda zai maye gurbin sa.

Manchester  zasu siya Neymar, zamu siyar- Barcelona

 

 

 

 

 

 

Kungiyar kafa ta Manchester ne ke kokarin mallakar dan wasan ta ko ta wani hali, Jarida Mundo Deportivo ta ruwaito cewa Manchester suna kokarin cimma matsaya ne dan asalin kasar Brozil din kafin ya amince ya sa hannu a sabon kwanataragi da ke jiransa a kungiyar Barcelona, wanda hakan zai sa kudin sakinsa ya hauhawa

Majiyar ta kara da cewa Manchester ta sabunta bukatar da take yi wadan wasan ne bayan Barcelona tayi watsi da tayin farko da ta ma dan wasan nap am miliyan 192. Sai dai dan wasan ya nuna shaukin sa na ci gama da zana a Filin wasa na Camp nou.

Kamar yadda wakilin Neymar ya bayyana, Neymar na jin dadi abin sa a Bacelona, amma duk da haka akwai wasu kungiyoyi da ke bukatar ganin sun siye shi. An dade ana watsar da zance sabunta masa kwantaragi, in da ake danganta shi da zuwa kungiyar PSG, Manchester har ma Real Madrid “Akwai wasu manyan kungiyoyi guda uku da ke neman siyan Neymar, kuma A shirye suke su biya Barcelona kudin sallama na euro miliyan 200” inji Riberio da yake zagzage ma Radio Jovem Pan labara.

Kamar yadda Jaridar Mundo Deportivo ta ayyana, kungiyar Barcelon sun yi ma Dan wasan tayin sabunta kwantaragi na karshe. Majiyar ta kara da cewa kungiyar kwallon ba zata mai karin albashin da ke kumshe a cikin sabon kwantaragin ba in dai don ta kau da bukatar da kungiyoyi irin su PSG su ka nuna ne.

Asali: Legit.ng

Online view pixel