Wata Mata ta ma yaro tsarki da barkono saboda N100

Wata Mata ta ma yaro tsarki da barkono saboda N100

-Wata mata ta ma wani dan shekara 7 tsarki da barkono domin ya sace mata N100

Wata Mata ta ma yaro tsarki da barkono saboda N100

 Yaron dan shekara 7 mai suna Razak Qudus, dan aji 4 ne a makaranta. Ya shiga halin ni 'yasu ne yayinda yayar shi mai suna Saratu ta shafa ma sa barkono a mazakutan sa domin tana tuhumarci da satan kudi N100.

Yaron Razak ya kasance yana zaune da yayar ta shi ne a Unguwar Afariogun, Oshodi a jihar legas.    An kai kayar ta shi Saratu ofishin yan sanda ne yayinda makwabta suka kai karanta wurin Shugaban kungiyar kare hakkin yara watau ‘Child Protection Network’, Ebenezer omelalile. Sai Ebenezer ta kai kara ofishin yan sandan Unguwar Makinde.

Game da Ebenezer omajalile ,Ta ce an kai Razak asibiti domin duba shi, ita kuma saratu zata gurfana a kotu. Ta ce: “Yaron dan uwanta ne. Yana zuwa wata makarantan firamaren kudi a unguwar Afariogun . An tuhumce shi ne da sace N100 a makaranta.  Matar ta shafa mai barkono a mazakuta. Yayinda muke ofishin yan sanda, na fada ma hukumar farga da zalunci na Jihar Legas da ke Unguwar Alausa. Na tabbatar da cewa sai an yi adalci a wannan al'amarin. Yaron na karkashin gwamnati a yanzu.

KU KARANTA : Wata mata ta ma yaro tsarki da barkono domin N100

Kakakin ofishin jami'an yan sanda na Jihar Legas,Mr. Dolapo Badmus, ya ce: “Abun zargin ta shafa ma yaron barkono a azzakari , sannan ta fara dukan shi. A garin haka yaron ya fadi kan risho ya kone da wuta a azzakarin sa. An kaita kotu kuma tana gidan yari."

Asali: Legit.ng

Online view pixel