Yan unguwa sun ma dan sanda lulus

Yan unguwa sun ma dan sanda lulus

- Yan zanga zanga sun ma wani dan sanda mai aiki a garin nsukka dukan rabani da yaro saboda ya kashe dan babur.

- Wasu ayarin yan sanda daga nsukka ne suka zo suka ceci rayuwarshi daga hannun mutane.

Yan unguwa sun ma dan sanda lulus

An samu wani tashin tashina  a jami'an Najeriya da ke Nsukka a ranar litinin , 28 ga watan yuni bayan ya aika wani dan babur lahira a bakin titin nsukka yayinda yake kokarin harbi sama. Jaridar Premium Times ta bada rahoton cewa hafsan dan sandan, wanda ake boye sunansa, yana aiki da Nsukka Building Material Taskforce wanda mai rikon kwaryan Shugaban Karamar Hukumar Nsukka, Rose Onah, ya nada.

Game da wani idon shaida ya ce: “An kashe dan babur din ne saboda yan taskforce kusan su 8 da yan sanda 4 na kokarin tilasta wani mai siminti ya biya kudin shiga da kaya.  Rokon da mai simintin ke yi ne yasa mutanen da zaune a wurin suka karaso domin rokon yan taskforce din amma suka kiya, idon shaida yace.

Da mutane suka taru sosai, sai yan sandan suka fara harbi sama domin tsoratar da mutane. Amma daya daga cikin yan sandan yayinda ya ke kokarin daga bindigar sa, sai ya bindige wani dan babur da ke fitowa daga gidan cin abinci. Wannan ya tayar da hankalin jama'an dake wurin, kawai sai suka hau dan sandan da duka , sai da ya fita daga hayacin shi. Amma daga baya, wata ayarin yan sanda sun zo daga ofishin yan sandan da ke nsukka, suka ceci rayuwarshi kuma suka dauke gawar dan babur din.

KU KARANTA : Yan’Najeriya basu amince damu ba, kwamishinan yan’sanda ya bayyana haka

Saboda tabbatar da tsaro, yan sanda suka fara fatrol a unguwar .Premium times ta ce. Baya ga haka, kwamishanan yan sandan Jihar Legas, Fatai Owoseni, ya bayyana cewa mutane ba su yarda da yan sanda ba, Jaridar Vanguard ta bada rahoto. Owoseni ya fadi hakan ne a wani taron da babban mai ba gwamnan jihar legas shawara akan harkokin cikin gari. Ya fadin hakan cikin yinkurin magana akan kashe kashen da yan bindiga keyi a unguwanni a Jihar Legas da Ogun.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng