Za muyi kintatawa a gidajen yarin Najeriya- Dambazau

Za muyi kintatawa a gidajen yarin Najeriya- Dambazau

– Ministan harkokin cikin gida, Abdulrahman Dambazau ya wata umurni zazzafa na gudanar da kintatawa a gidajen yarin Najeriya

–Dambazau ya ce  Komftrola Janar na hukumar gidajen yarin Najeriya ne zai gudanar da kintatawan

Ministan harkokin cikin gida, Abdulrahman Dambazau ya wata umurnin kar ta kwana na kintata dukka gidajen yarin da ke kasar Najeriya gaba daya.

Za muyi kintatawa a gidajen yarin Najeriya- Dambazau
Abdulraman Dambazau

Yayinda yake Magana a ziyarar da ya kai gidan yarin kuje a babban birnin tarayya  Abuja,inda firsunoni 2 da ke sauraron gurfana  suka balle , Dambazau yace sai an gudanar da shi da wur wuri a dukkan kurkukun kasa gabaki daya. Komftrola Janar na hukumar gidajen yarin Najeriya, Peter Ekpendu, ne zai tashi da aikin kintata gidajen yarin.

A wata jawabin da mai Magana da yawun Ministan harkokin cikin gida, Osaigbovo Ehisienmen ya bayar, ya ce ba zamu yarda da ballewan firsunoni 2 daga gidan yari ba. Osaigbovo Ehisienmen yace Ministan ya bada umurnin a dau dukkan mataki na tabbatar da cewan hakan ba zai sake faruwa ba.

Game da kuma abinda ya faru har wasu suka arce daga gidan yarin, dambazau ya nada kwamitin bincike cikin al’amarin. Ya kuma umurci Komftrola janar na hukumar gidajen yarin najeriya,cewa ya hada kai da hukumar yan sanda, ma’aikatar shiga da fice, hukumar yan sandan asirce,da wasu jami’an tsaron da zasu taimaka wajen kamo wadanada suka arce da wuri.

KU KARANTA : Mutane 2 da Suka Gudu daga gidan Yarin Kuje

A ranar  asabar,25 ga watan yuni, firsunoni 2 sun balle daga gidan yari da ke kuje,a Abuja. Firsunonin da suka arce na sauraron gurfana ne da laifin kisan kai

Asali: Legit.ng

Online view pixel