Masu sana'ar hannu a Najeriya sun sana'arsu da 60%
-Ba wani Sabon labari bane cewa tattalin arzikin Najeriya ya shiga halin kaka nikayi.
-'Yan Najeriya suna Jin jiki daga abubuwa ukku da wannan shiga kaka nikayi da tattalin arzikin ya shiga.
-Masu sana'ar hannu na bangarori da yawa na tattalin arzikin kasar sun yi Karin ladar sana'unsu na fitar hankali.
Wani rohoto da Ventures Aftica ya ruwaito na bayanin yadda masu sana'ar hannun suka rubanya ladar sana'unsu gida uku sanadiyar shiga kaka nikayi da tattalin arzikin kasar wanda shine mafi girma a Afrika da Yamma yayi. Masu aiki bangaren gine-gine sun yi kari na kashi 60% dalilin tashin farashin kudin petur da kayan abinci.
Rohoton ya cigaba da cewa kwararrun masu aikin hannun irin su kafintoci da magina sun kara ladar ayyukansu daga N3000 zuwa N5000 a kowace rana, karin da ya kama kashi 66.6%, yayin da wadanda basu kware ba ladar ayyukansu ta tashi daga N1000 ko N1500 zuwa N2000 a yini.
Masu sana'ar hannun suna fama da halin kaka nikayi da tattalin arzikin kasar ya shiga.
"Ladar masu sana'ar hannun ta karu da kashi 25% zuwa kashi 60%, ya danganta ga irin ma'aikacin da kake so. A kwai kwararrun leburori, akwai kuma wadanda basu kware ba. Kwararren labura zai amshi N2000 a yini wanda bai kware ba kuma N1000 ko N1500 a yini" .cewar tsohon shugaban kungiyar injiniyoyi ta sashen jihar Lagos Olatunde Jaiyesinmi. Tashin farashin kayan abinci da man petur sun jawo tashin farashin kayayyaki a cikin kasar na kashi 15.1% a cikin wannan watan, cewar rohoton da hukumar da ke kula da dakiku na kasa wadda ake Kira National Bureau of Statistics (NBS).
"Ba Kari bane wanda aka zauna aka yarda da shi ba, kari ne wanda ya faru Kai tsaye dalilin tashin farashin kayayyaki a cikin tattalin arzikin kasar. Kudin sufuri da na petur, duk sun tashi, saboda haka kudin komi ma ya tashi, har da kudin abincin da lebura zai ci", cewar Kunle Awobodu, mukaddashin shugaban hukumar dake kula da magina wato Nigerian Institute of Builders.
KU KARANTA : Ku gano yadda masu kasuwanci a kasar China maraba Shugaba Buhar
Janar sakataren na kungiyar birkiloli ta sashen jihar Lagos yace kungiyar bata bada umurnin Kari ba saboda yana ganin tattalin arzikin zai inganta cikin dan karamin lokaci.
Asali: Legit.ng