Abinda Maradona ya fada ma Messi
Shahararren dan Kwallon kafar nan dan kasar Ajantina wato lionel Messi ya sanar da murabus din sa daga harkan buga kwallon kasa da kasa. Sai dai sanannen tsohon dan kwallon Ajantina Maradona ya bai wa Messi shawara da kada ya cika alwashin san a daina doka wasan kasa da kasa. Ana ganin wannan shine wasan karshe na hudu da Messi ke jagorantar yan wasan amma ba’a samun nasara.
Shi dai kyaftin din Ajantina Messi yayi murabus dinne biyo bayan kayin da suka sha a hannun kasar Chile a wasan karshe na gasar cin kofin nahiyar Amurka wanda aka buga a kasar Amurka. Kamar yadda ta cinye a shekarar 2015.
Kungiya kwallon kasar Chile da ake ma lakabi da La Roja ta rike Ajantina ne har tsawon mintuna 120 ba ci, wanda haka ta kai su bugun daga kai sai gola. Lucas Biglia da Messi ne suka barar ma Ajantina da kwallaye, in da shi kuma Aturu Vidal ya barar ma Chile.
Kasancewar Lucas Biglia shine na hudu a jerin mabugan Ajantina, barar war da yayi yasa Francisco Silva ya ci kwallon da ya ba Chile nasara cin kofinta na biyu kacal a tarihinta. Bayan shan kayen ne, Messi dan Barceloan ya ce “Na gama da kungiyar kwallon kasa ta”
Wannan shine rashin nasaran mu na hudu, ba nawa bane kadai. Na riga na yanke shawara “ina jin zafin abin har yanzu, na barar da bugun daga kai sai gola, kuma shine abu mafi muhimmanci. shikenan”
Sai dai Diego Maradona ya fadi cewa “Ya kamata Messi ya ci gaba da wasa da kungiyar kasar sa, zai tafi Russia yana mai karsashi, zai zama zakara a can. Ya kamata ya zama mai kulawa ne day an wasan da zasu iya taimaka ma kungiyar, ba wai yan wasa masu cewa zasu tafi ba”
Ya kara da cewa “ma su cewa ya daina wasa, suna fada ne domin kar mu gane mtsalar dake tattare da harkar kwallo a Ajantina, na yi matukar tausaya masa, kuma ina bakin cikin irin yadda lamarin kwallon Ajantina la tabarbare. Mun dafa kasa.”
Asali: Legit.ng