Rooney ya bayyana kalaman Kocin sa

Rooney ya bayyana kalaman Kocin sa

Kasar Ingila dai ta kwashi kashinta ne a hannun makwabtan su kasar Iceland. Wayne Rooney dai ya bayyana kalaman kocin bayan an tashi wasa, Kyaftin din ya kuma yi bayani game da kayen da suka sha mafi muni a tarihin kasar gaba daya. kayen da Ingila ta sha a hannun karamar kasa Iceland 2-1 a zagaye na 16 ya nuna kenan an fatattake ta daga gasar cin kofin nahiyar Turai na 2016.

Rooney ya bayyana kalaman Kocin sa

 

Wayne Rooney shine ya fara ci ma Ingila kwallo, inda ya jefa kwallo a raga da bugun daga-kai-sai-gola minti hudu da fara wasa. Amma murna ta koma ciki bayan mintuna biyu lokacin da Ragnar Sigurdsson ya farke kwallon, sa’annan bayan mintuna 19 dan wasan gaba na Iceland Kolbeinn Sigthorsson ya buga wata kwallo da Golan Ingila Joe Hart ya gagara kamawa, inda ka tashi 2-1.

A yayin da yake Magana bayan an kare wasan, Rooney y ace “Na yi matukar bacin rai, ba abu bane mai sauki. Mun samu damanmaki da yawa a lokacin da muke taka leda da kyau, amma sai an ci mu kwallaye biyu masu arha, cin ya bata mana rai.” Da yake bayanin yadda Roy Hodgson ya fada musu shirin sa na murabus, Rooney yace “sai a bayan wasa ya fada mana, sai da duk ya zagaye gaba daya yan wasan, mu kam a mtsayinmu na yan wasa, mun gode da duk abin da yayi mana, ya baiwa yawancin sabbin yan wasa dammar buga ma kasar su a karin farko, kasan ba zaka taba manta hakan ba”

Tauraron kungiyar kwallo ta Manchester Rooney ya ci gaba da cewa “ina ganin ba dadi ganin abin da ya faru a yanzu, amma akwai nasara a gaba, tuna wannan ranar zai yi mana zafi, kuma zai dauki lokaci kafin mu manta, amma dole muyi kokarin cire shi a rai mu ci gaba da rayuwarmu”. Ya kara da cewa “na fada tun kafin a fara gasar, ina alfahari da bugawa Ingila da nake yi, yanzu ina jimirin in ga wani sabon Koci za’a kawo mana, kuma idan ya zabe ni don buga wasa, kofa ta abude ta ke”

Asali: Legit.ng

Online view pixel