Sabon Sifeto Janar zai ma manyan yan sanda 30 ritaya

Sabon Sifeto Janar zai ma manyan yan sanda 30 ritaya

-  Sabon sifeto janar na yan sanda yace  tsige wasu manyan jami’an yan sanda

-  Manyan jami’an yan sandan sun yi kokarin ganawa da shi amma basu samu ganin shi ba.

-  Wata majiya ta ce manyan jami’an na daga cikin kwararrun yan sandan da kasan nan ke da shi.

-   An samu rahoton ne ta wata wasikar da sabon sifeto janar na yan sanda, Ibrahim Idris, ya rubuta.

Game da Jaridar Thisday, sabon Shugaban yan sandan ya rubuta wata wasika zuwa ga shugaban kasa, Muhammadu Buhari, a ranar 24 ga watan yuni , ya na neman izinin ritayan manyan jami'an yan sanda 30.  Idris ya zama sabon sifeto ne sanadiyar karewar wa'adin tsohon sifeton , Solomon Arase. Jim da kadan da hawa ragamar mulki,ya nemi ritayan mataimakan Sifeto Janar guda 6 da sukayi aiki karkashin Arase.  An nemi ritaya manyan yan sandan ne saboda frotocol din sabon Sifeton Janar din yan sandan da ya hau ragamar mulki.

Sabon Sifeto Janar zai ma manyan yan sanda 30 ritaya
sabon igp

An bada rahoton cewa manyan jami’an yan sandan sun nei ganawa da sabon Sifeton yan sandan amma an hana su.

Wata majiya tace:

“ Akwai tashin hankali a hedkwatar yan sanda a Abuja. Mu samu labarin cewa sabon Sifeton ‘yan sanda na son yayi ritayan manyan shi da abokan aikin shi. A ranar juma’a, ya rubuta wasika zuwa ga shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa ,Abba Kyari, kuma ya yarda da ita,ya aika teburin shugaban Kasa domin sanya hannu.

Game da abinda Ibrahim Idris ya rubuta, dalilin shin a yin hakan,shine ba zai iya aiki da su ba.  Ya ce tunda ya hau ragamar mulkin samarda tsaro a wannan kasan, to yanada muhimmanci a cire wadannan AIG’s din, saboda za su iya zama mai cikas a wurin samun nasara. saboda Wannan yunkurin, akwai yiwuwar kara wa kwamishinoni 14 girma zuwa AIG kenan tunda ana akwai kujeran AIG 26 . Kafin yanzu, an karawa AIGs 12 girma, daga cikin 12, za'a karawa 7 girma zuwa DIG. saboda haka, dole a samo kwamishinoni su maye gurbin AIG 26.

KU KARANTA: Buhari ya yi kuskure a nadin shugaban ‘yan sanda –NOPRIN

Muna mamakin abinda yada ake bukatan cire kwararru da zasu taimaka masa wajen cigaban yan sanda. Wadannan manyan da za’a cire, sune manyan karshe a ofishin yan sandan da aka turo horo kasar waje kuma sun yi kwasa kwasai. Ban san me yasa ake son asaran mutane bs. Idan aka cire su, dole dai mun kashe makudan kudi domin horar da sabbin AIG da kwamishinoni.

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel