Gwamnatin tarayya zata tura Kwararrun Sojoji Neja Delta
Ana tunanin Gwamnatin tarayya zata tura wasu Sojojin da suka fafata a yakin Boko haram da ke gudana a Arewa maso Gabas zuwa Neja Delta domin su yi maganin miyagun ayyukan Tsagerun Neja Delta
Sojojin za su kasance daga cikin sabuwar Rundunar kawo zaman lafiya a yankin wato ‘Operation safe Delta’. Nan bad a dadewa ba ake sa Gwamnatin Tarayya zata bayyana matsayinta game da sharuddan da Tsagerun yankin Neja Delta suka gindaya mata sanadiyyar ci gaba da miyagun ayyukan da suke tafkawa.
Rohotonni sun nuna cewa Sojojin za su kasance cikin sabuwar Rundunar kawo zaman lafiya yankin da ked a hedikwata a a Birnin Yenagoa, kuam za’a tsarata ta kasance gida uku, da kuam raberaben aiki guda biyar don ta mamaye dukkanin yankin Neja Delta.Darektan wucin gadi na Hukumar Soja, Birgediya Rabe Abubakar ya ce Hukumar Soja zata tabbatar da ingancin kayan aikin wannan sabuwar Rundunar domin ta samu damar cimma manufan kafa ta.
“Gyaran fuskan da aka yin a nufin samar da kuzari ne ga sabuwar Rundunar. Zamu cigaba da kawo sabbin tsaretsare, sabbin kayan aiki da kuma sabbin hanyoyi gwargwadon iko, don hana faruwar abubuwan da suka faru a baya, hakan yasa Hedikwatar tsaro ta kakalo wannan gyaran fuska, wadannan matakan duk don tsaron Kasa ne da kuma kamfanonin da ke can”
Ya kara da cewa “Muna ta kokarin ganin mun yi iya kokarin mu da mafi kyawun Makaman mu, mafi kyawun Kayan aikin mu don mu yi maganin duk wani baraza ga zaman lafiya. Amma a sani, kawo sabbin Makamai, da sabbin Jami’an Soja ba shine abin dubawa ba, Abu mafi muhimmanci shine an gudanar da Gyaran fuskar ne domin amfanin Kasar ne gaba daya, domin amfanin Yankin gaba daya. Za mu yi bakin kokari mu tabbatar mun tsare dukkanin wurare, Jami’an mu, Kayan aikin mu da duk abin da muke da don ganin cewa an yi aiki yadda ya kamat ” in ji shi
A bangare guda kuwa, ba da dadewa ba Gwamnatin tarayya zata bayyan matsayarta game da sharuddan da Tsagerun Neja Delta suka gindaya mata idan ana son zaman lafiya a yankin. “nan ba da dadewa ba ne Gwamnati zata sanar da ko ma wani irin matsayi ta dauka. Amma b azan iya fada muku tabbataccen Magana ba”
“Zancen zai fito ne daga bakin Gwamnati, wannan ba karamin magana bane, soboda haka ba wai irin zancen da kawai mutum zai zauna bane ya fadi, ya shafi kowannen mu. Saboda haka ba kawai matsalar Ma’aikatan mai bane ko NNPC, abu ne day a shafi kowannen mu, saboda haka Gwamnati na duba maganar” in ji mai Magana da yawun NNPC, Garba-Deen Mohammed yak e ma manema labarai bayani Lahadin da ta gabata a Abuja.
Shi ko Gwamnan Jihar Bayelsa Seriake Dickson, ya bayyan vewa sulhu kadai ka iya maganin matsalar Neja Delta. In ji Gwamnan “Dukkanin mu muna son ci gaba; Dukkanin Shuwagabannin da kenan su nuna damuwarsu akan ta’addancin da ke faruwa a yanzu. Muna hadin gwiwa akan yadda za’a magance matsalar. Gwamnonin cikin na kokari tare da Shuwagabannin gargajiya, Shuwagabannin Al’umma da kuma Jami’an Tsaro, kuma hadin gwiwa da kungiyoyi masu zaman kansu don mu tabbatar mun sanya ma matsalar Linzami. Yaki ba shine mafita ba, tattaunawa shine. Mafita a nan shine sulhu da zaman lafiya, shine abin da muka yi yarjejeniya a kai, kuma muke goyon baya”
Ya kara da cewa “Ba ma goyon bayan tashin tashina; bamu goyon bayan Tsageru. Ba ma goyon bayan lalata kadarori da kashe kashe. Mun san akwai matsala, kuma matsalar za’a iya magance ta idan duk masu ruwa da tsaki sukayi himma akan Hadin kai, luman da kuma ci gaba mai dorewa na wannan kasa ta mu. Ya ce, a halin da ake ciki, tasagerun yan Asalin kasar Biafra-IPOB sun kaddamar da Kalmar ‘BIAFREXIT’ a matsayin taken su.
Asali: Legit.ng