Belgium ta tsallake zuwa Zagayen na biyu

Belgium ta tsallake zuwa Zagayen na biyu

Belgium da Jamani sun tsallaka zuwa zagaye na biyu a Gasar cin kofin Kwallon Nahiyar Turai

Belgium ta tsallake zuwa Zagayen na biyu
Yan wasan Belgium

Belgium ta kafa tarihin zura Kwallaye mafi yawa a gasar cin kofin nahiyar Turai na bana 2016, za su hadu da Wales a zagaye na gaba wato ‘Quarter final’. ita ma kasar Jamani ta lallasa Abokiyar karawanta ne ci 3-0. Belgium dai ta baiwa Abokiyar karawarta Hungary ne mamaki a yayin da ta yi bijibiji da ita, kuma ta fitar da ita daga gasar, wanda haka ya sa zata hadu da Wales a zagaye na biyu.

Dan wasan kasar Belgium Toby Alderweireld da ke taka leda a kulob din Tottenham dake Ingila ne ya fara bude was da cin kwallo, daga nan sai Michy Batshuayi, Eden Hazard da kuma Yannic Carrasco suka zura kwallaye a bayan an dawo hutun rabin lokaci. Haka yasa wasa ya kare a matsayin Belgium 4, Hungary 0.

Yanzu dai ta tabbata Belgium zasu hadu da Wales a fagen fafatawa don nuna kwanji tsakanin kasashen biyu. Idan ba’a manta ba, kasar Wales ta taba lallasa kasar Belgium a zagayen wasannin fidda gwani da aka buga domin cancantar zuwa gasar da ake bugawa a yanzu, duk ko da tarin sanannun yan wasanta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel