Ramadan: Abubuwa 5 masu muhimmanci a 10 karshe

Ramadan: Abubuwa 5 masu muhimmanci a 10 karshe

Kashi 2 bisa 3 na kwanakin Azumi sun wuce, Muslmai yanzu suna cikin kwanakin 9 ko 10 karshe na Azumin bana shekara ta 1437 bayan Hijira, ya danganat da kwanakin da watan za ta yi, 29 ko 30. Kwana 10 karshe na wannan wata mai tsarki yana da muhummanci sosai da sosai, Kasancewa Mutum na Azumin awa 14 a garuruwan Legas, Ogun, ko kuma Oyo ba wasa bane, balle ma Musulman da ke Azumi a kasashen Turai da wasu kasashen da basa ganin dare, wadandan sukan yi Azumin awa 20 ne zuwa 23.

 

Hakan na nuni ga cewa duk Muslmin da gudanar da Azumin sa cikin kiyaye dukkanin ka’idodin da aka gindaya mai to ya kamata ya zage damtse domin ya ribaci gagarumar riba a wadannan kawanki 10 na karshe. Daya daga cikin dalilan da yasa aka fi bada Muhimmanci a kan goman karshe shine daren Lailatul Qadari ta kan fado ne a cikin wadannan kwanaki na watan Ramadana.

Ka kara kaimi a karanta Al-Qur’ani

 

Idan ya kasance Musulmi ya kan karanta shafi 10 zuwa 30 na Qur’ani mai tsraki ne a kowane rana, toh ya dage ya kara daga shafi 30 zuwa 80 har ma 100. Dalili kuwa shine gwargwadon karatunsa gwargwadon ladan sa. Bugu da kari ma, a wadannan kwanaki 10 ne aka saukar da Al-Qur’ani.

Tsuyuwan Tahajjud

 

Sallar Tahajjudi wata Sallace da akeyinta a tsakiyar dare idan an farka barci, ya kamata aba wannan Sallar muhimmanci. Idan da kana yin raka’o’I hudu ne a Tahajjud, to ka dage ka ninka shi zuwa 8 ko sama da haka. Kada a manta, ita Sallar Tahajjud ana yin ta ne biyu biyu kamar 2, 4, 6, 8, 10. 12, haka dai.

Yawaita Addu’a

 

Musulmi y adage da yawaita yi da kuma maimaita Addu’ar da Annabi ya umarci Musulmai su yi, it ace “Allahumma Innaka Afuwwun, Tuhibbul Afwa, Fa’afu annee”, Addu’ar tana nufin “Ya Allah, Kai ne mai gafara, Kana kaunar yin gafara, Ka gafarta

mini”. Ana so Musulmi ya yawaita maimaita wannan Addu’an Safe, Rana da Daddare.

I’itikafi

 

I’itikafi na nufin tarewa a Masallaci na tsawon wasu kwanaki da nufin bautan Allah sosai da sosai. An so idan ma za’a samu dama, toh a kwashe gaba daya kwanaki 9 ko 10 duka a cikin Masallaci. Amma idan misali hidimar yau da gobe ba zasu bari Mutum ya tare gaba daya kwanaki 10, toh zai iya raya dararen wadannan kwanakin.

Sadaka

 

Sadaka ta kunshi ciyar da Miskinai da masu karamin karfi, bayar ma Mutane kyautan kudi, ko kuma ka kashe kudi wurin yi ma Addini hidima, kamar gyaran Masallaci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng