Buhari yaba yan Najeriya kunya- Yerima Shettima
Yerima ya tofa albarkacin bakinsa game da Gwamnatin “Mutane sun sa rai sosai a wannan Gwamnatin, saboda yayi (Buhari) alkawarin kawo canji ne, amma kash ba zai iya tafiyar da kasar nan shi kadai ba. Wasu daga cikin ministocinsa ma basu da kwarewa da sanin makamr aiki, basu san yadda ake tafiyar da mukli ba, ban gamsu da kamun ludayin wannan Gwamnatin ba, yan Najeriya suna kokawa. Babu yadda za’a yi ka dauke dukkan jin dadin da Mutane ke amfanuwa das hi, kuma ka ce mu yi murna. Abubuwa sun yi kamari, baka da dammar yawon duniya, kuna talaka na cikin kunci, su Shuwagabanni ya kamata su fara zage damtse kafin talaka”
“da yawa daga cikin Mutanen da suka mara masa baya ma sun koka, harta ma Canjin da ake cewa, duk Mutane sun watsar. Gwamnatin ta kasa cin ma yawancin abubuwan da ta alkarwanta, amma ta bige da yin abubuwanta gaba-gadi ”
Game da 2019 kuwa, ya kara da cewa “Buhari Shugaban Najeriya ne ba na wani bangare daya ba, da ace muna gudanar da tsarin Gwamnatin yanki ne, toh dab a zan soke s ba, sai dai kawai in basa shawara.”, akan batun ko ai mara wa Buhari baya sai y ace “Za mu nemi wani dan takarar a 2019, Gwamntin nan ta bamu kunya da yadd take tafiyar da al’amuran ta, saboda haka yadda al’amura suke wakana Gaskiya 2019 sai mun nemi mafita”
Game da nadin da Bihari yayi, Yerima y ace “Shugaba kasa bai yi ma wasu bangarori adalci da fari, amma kaga tun da aka fitar da bajet, abubuwa sun daidaita. Dole mu yabe shi a bisa haka. Kaga har ma nadin ambasadodi da yayi, mutum nawa ne yan arewa a cikin su? Haka nadin Shugabannin hukumomi. Daga Bajet ma kawai zaka fahimci Kudu maso yamma ta fi arewa ma da kashi 40, sai ya fi yi ma Kudu maso Yamma amfani fiye da Arewa maso Gabas in da na fito da ta ked a kasa da kasha 13, daga farko ba adalci, amma yanzu an gyara, kuma na daga muryana akan haka a baya”
Game da Yaki da Almundahana da Shari’ar Dasuki, ya ce “Ohishin mai bada shawara aka harkokin tsaro ba wai ofishin PDP bane, wasun mu muna shakkar irin tsarin Yakin da ake yi da cin hanci da rashawa, kuma mun fada haka tun a tashin farko. Bai kamata ace Shugaban kasa yana sa baki akan aikin Hukumomi ba, Shugaban ya riga ya sa a ransa ba zai saki Dasuki ba saboda ya saci sama da biliyan 400, kamar yanda ya fada a hirar da yayi day an Jaridu, kamar ma ya yanke masa hukunci ne. Bai kamata ba tun dab a kotu bace ta kama sad a laifi, balle a lokacin da kotu ta bada dammar sakin sa, kuma a gaskiya duk Shugaban da ke taka izinin kotu ba Adali bane. Sabod abin dake faruwa yanzu zai iya faruwa akan kowa”
a kara da cewa “Yayi yaki da Almundahana, saboda ko bayan ya tafi, hukumomin zasu ci gaba da aikin su yadda ya kamata. Muna goyon bayansa akan yaki da rashawa amma fa kada ya kasance akwai wata manufa ta daban a cikin ta”
Asali: Legit.ng