Ben Bruce ya bayyana Jihohin da suka waye a Najeriya
-Sanata Ben Bruce ra bayyana jahohin da suka waye a najeriya.
-Ben bruce yace jahar Adamawa, Ribas, Imo, dakuma Edo sune jahohin da sukafi wayewa a najeriya.
-Yayi amfani da cigaban da suka samu wajen auna mizani.
-Ben murray bruce yace yana son yayi amfani da hankali.
Sanatar da yayi fice a kafar sadarwa yace shekaru ashirin da suka wuce kudancin kasan nan sune koma baya a tabarbarewan harkan illimi wanda hakan ya sanya yaran basa kokari ko kadan a makaranta, yanzu kuma suke kan gaba wajen jarabawar WASSCE.
Ya fahimci jahohin Abiya, Anambra, Ribas, da kuma Imo sune suka zo na daya dana biyu dana uku dana hudu da biyar ajerin.
Sanata bruce yace jahar edo itace jaha ta uku a cikin jerin jahohin.Sanata Bruce yace yakamata gwamnatin tatayya dama saurin jahohin kasar nan su lura da abunda sukeyi mai kyau domin ayi koyi dasu.
KU KARANTA: Ben Murray-Bruce, Kamantawa, ko ci da buguzun?
Da yake fadin hakan a shafinsa na facebook, bruce yace abunda ya faru a yankin na kudu abun al'ajabine, mussamman idan akayi la'akari da dan kudin da ake basu daga gwamnatin tarayya na aiyuka, amman duk da haka sun samu damar aiwatar da wannan gagarimar nasarar da fannin ilimi dakuma tattalin arzikin kasa.
Asali: Legit.ng