Ramadan: Abubuwa 5 da ya kamata magidanta su kiyaye
Watan Ramadan wata ne da ya kamata magidanta su kyautatawa iyalansu; wadannan shawarawari su za su taimaka wajen ganin an yi hakan:
KU KARANTA: Dokar Hana Addini ta Sabawa kundin tsarin mulki – Osinbajo
Cin abinci da jama’a na sa kauna da son juna. Ballantana a tsakanin iyali, yana da kyau magadanta su rika yin sahur da buda baki tare matansu da ‘ya yansu a wuri guda.
Karatun al Qur’ani a watan Ramadan na da falala mai yawa, don aka yana da kyau magidanta su rinka karatun Qur’anin da iyalan su domin samun albarka da kuma lada mai yawa.
Ramadan wata ne da ake nunka ladan musulmi idan ya yi aikin alheri, haka ma idan ya aikata ba daidai ba. Yana da kyau mu hori iyalan mu da aikata kyakkyawa tare da hana su aikata mummuna a wannan watan.
Yana da kyau a karafawa yara da shekarunsu ya kai (10 zuwa 14), da su yi azumi. Idan sun dauka kuma a karfafa musu gwiwa a ga sun kai. Komai wahala in har sun dauka to kar a bari su karya. Yana da kyau a yaba musu in sun kai azumin. Haka zai sa su saba kafin su balaga.
Ramadan wata ne na kyautatawa da farantawa juna. Yana da kyau magidanta su kyautatawa matan su ta hanyar da duk ta dace. Yara ma haka.
Asali: Legit.ng