Zenith Bank sun zo bani hakuri - Fayose
- Gwamna Ayodele Fayose ya bayyana cewan manyan ma’aikatan bankin Zenith sun kawo mai ziyara domin bashi hakuri akan abin da ya faru na kudin da EFCC ta daskarar a bankin su
- Amma, shugaban bankin Zenith din ya fadi akasin haka, yace sun kai masa ziyara ne kawai
Gwamna Ayodele Fayose na Jihar Ekiti ya bayyana cewa manyan ma’aikatan Jihar Ekiti sun kawo mai ziyara da yammacin yau, alhamis 23 ga watan yuni. Sun zo ne domin bashi hakurin sa hannun bankin cikin yakin zaben 21 ga watan yuni ,shekarar 2014. Sun kai ziyarar ne bayan sun karyata cewa bas u cikin wadanda suka yi yakin zaben.
Direktan bankin Zenith,Sola Oladipo ne tare da wadansu direktocin sashe 2 da manajan sashen Ado-Ekiti ne suka kai ziyarar. Fayose cikin maganarsa ,yace ma’aikatan bankin sun zo bashi hakuri ne akan abin da ya faru.
KU KARANTA: EFCC na tuhumar jami’an NNPC a gaban kotu
“ Sun zo suna bani hakuri wai kada abin ya wuce haka,nace musu me yasa suka je suka fada wa EFCC karya. Me yasa su kayi karyan cewa kudina daga ofishin mai ba shugaban kasa shawara ne akan tsaro/ idan kudin nawa ne,me yasa suka hada ni da abinda bas hi ba,” mai Magana da yawun sa ya yada. Amma direktan bankin yace sun kawo ma gwamnan ziyara ne kawai.
A ranar litinin ne ,20 ga watan yuni, hukumar EFCC ta daskarar da asusun bankin guda 2, daya na Ayodele Fayose,daya da kamfanin sa. Ana tuhumar sa da amsan biliyan 4.7 daga ofishin sambo dasuki a lokacin yakin neman zaben sa a 2014.
Fayose ya karyata hakan,yace bai amsa kudi a hannun kowa ba.
Asali: Legit.ng