Auren Mikel Obi da Hajara Saleh ya zo da tangarda

Auren Mikel Obi da Hajara Saleh ya zo da tangarda

-Shirye-shirye sun yi nisa na daura auren fitaccen dan wasan da Hajara Saleh Barde a Kaduna.

-sai dai daurin auren Mikel Obi ya ci karo da wasanninsa na Chelsea

-Fusataccen dan wasan ya zargi ejansa da sa wasa a ranar daurin aurensa.

 Kyfatin din ‘yan wasan Super Eagkes na Najeria na cike da fushi da ejansa, saboda sa ranar aurensa daidai da lokacin da Chelsea ke wasanninta na sada zumunta.

Auren Mikel Obi da Hajara Saleh ya zo da tangarda
John Obi Mikel na shirin zama ango

Babawo Mohammed ya ce laifin na iyayen amarya ne, da suka kai daura auren ranar 30 ga watan Yuli, wanda hakan ba zai ba fitaccen dan wasan damar halartar daurin aurensa da Hajara Saleh Barde ba, wanda aka shirya za’a yi a Kaduna. Dalili? hakan ya ci karo da wasannin sada zumunci da kulop din sa Chelsea ke yi a karshen gasar Euro 2016 a ranar 10 ga watan Yuli.

Baya ga wasanninsa da Chelsea na gabannin kakar wasanni, Mikel zai shiga shirye-shiryen zuwa gasar Olympics da ‘yan kasa da shekaru 23 na Najeriya, wanda za’a soma ranar 4 ga watan Agusta.

KU KARANTA: Eyimba ta nada sabon mataimakin koci

A hirar sa da shafin Owngoal.com na intanet, Mohammed ya na mai cewa: “Mikel na fushi da ni, amma ba ni na sa ranar bikin ba, babu kuma yadda zan yi saboda iyayen amaryar ne suka yi hakan, nima zan so a ce ya zo daurin auren da kan sa.”

Har yanzu dai ba’a tabbatar da cewa tsohon dan wasan Lyn Oslo din zai samu zuwa daurin auren ba, ko kuma iyayen amaryar za su daga daurin auren zuwa lokacin da zai iya halarta da kan sa.

     

Asali: Legit.ng

Online view pixel