Tofa!: Ibrahimovic zai bar bugama kasar sa kwallo

Tofa!: Ibrahimovic zai bar bugama kasar sa kwallo

Shahararren dan kwallon nan dan kasar Sweden Zlatan Ibrahimovic ya bayyana aniyar sa na barin yi wa kasar sa kwallo bayan an gama gasar cin kofin kasashen turai da akeyi yanzu.

Tofa!: Ibrahimovic zai bar bugama kasar sa kwallo
Zlatan Ibrahimovic

Ibrahimovic ya bayyana ma yan jarida hakan ne kafin wasan su da Belgium. Ibrahimovic din ya ce: "Wasan da zan buga na karshe a wannan gasar shine wasa na na karshe da kasar tawa. Bazan buga gasar Olympics ba. Don hakan wannan gasar itace ta karshe a gareni. In fatan zamu dade a gasar, zamuyi nisa. Bani da wata nadamar yin hakan kuma".

Ibrahimovic din ya kara da cewa: " Ni fa bani da wata nadama, ina alfari da yadda nayi wa kasata kwallo inda har na jagorance ta. Inaso kuma inyi anfani da wannan damar don gode ma magoya bayana a duk tsawon shekarun nan kuma a duk inda naje. Zan cigaba da alfahari da kasata kuma zan cigaba da kare martabar ta."

Ku karanta: Wani ya kashe matarsa saboda N100

Yanzu da haka dan kwallon na daf da komawa kulob din Manchester united bayan rahotanni da dama sun bayyana cewar ya aminci da kwantaragin shekara daya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel