Gwamnan Abia ya koka da rashin kudin yin zabe

Gwamnan Abia ya koka da rashin kudin yin zabe

-Gwamna Okezie Ikpeazu ya ce jiharsa ta tsiyace har ta kai ga cewa ba za ta iya gudanar da zaben kananan hukumomi ba.

-Gwamnan Abian ya koka da rashin gyara manyan wani babban titin a babban birnin jihar saboda fatara

-Ya umarci kananan hukumomi da su nada nakasassu a mukamai domin nunawa jama’a cewa gwamtaisa ba ta kyamar kowa.

Gwamnan jihar Abia Okezie Ikpeazu ya ce jiharsa ta fada cikin fatarar da ba za ta ita gudanar da zabukan kananan hukumomi ba. Wannan, a cewarsa shi ne babban dalilin da ya sa jihar ba ta yi zabukan ba, saboda ba za ta iya kashe zunzurutun Naira miliyan 800 ba don gudanar da zabukan.

Gwamnan Abia ya koka da rashin kudin yin zabe

KU KURANTA: Watan Ramadana:Shin Musulmai nawa ne suka iya wannan?

Hakan ta fito fili ne a yayin wani gangamin taron jama’ar gari na mazabar sanata ta kudu a Obehie a Ukwa da kuma makarantar fasa ta Abia da ke Aba. A lokacin ne gwamnan ke cewa; “wata uku ke nan ina tambayar hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar da ta ba ni lissafin a bin da zaben zai ci, sai ta ba ni lissafin Naira milyan 800.”

Gwamnan ya kara da cewa babu yadda zai yi ya samar da wannan kudi domin gudanar da zabukan, don haka sai dai a san dabarar da za’ayi.

Wannan ne ma ya sa ya gaza gyara wasu hanyoyin a babban birnin jihar, sai dai an kulla wata yarjejeniya da Bankin Duniya na gyara wata babbar hanya kafin ya hau mulki, za’a kuma soma aikinta nan ba da dadewa ba.

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel