Fulani Makiyaya sun haddasa gudun hijira a Benue
Wasu mazauna wani gari da ake zargin cewa Fulani makiyaya sun kai ma hari a Jihar Benue inda hotunan ke cigaba da zagaye shafukan sada zumunta a yanar gizo kamar wata gobarar daji.
Wasu mazauna wani gari da ake zargin cewa Fulani makiyaya sun kai ma hari a Jihar Benue inda hotunan ke cigaba da zagaye shafukan sada zumunta a yanar gizo kamar wata gobarar daji.
Jaridar The Breaking Times ta ruwaito cewa mutanen suna barin kauyukan su ne inda suke tafiya nenza dake a karamar hukumar Logo, zuwa Tudun na tsira dake a cikin jihar ta Benue. Acewar jaridar, mutanen suna barin kauyukan nasu ne saboda suna kokarin guduwa daga hare haren da Fulani makiyaya suke kaimasu a cikin gidajen su.
Majiyar jaridar ta bayyana cewa masu gudun suna rugawa ne zuwa hedikwatar karamar hukumar ta Ugba, inda wasu daga cikin su sun share kilomita 16 zuwa 30 kafin su isa garin na Ugba. Anyi kira ga gwamnatin tarayya data jiha data kawo karshen wannan mummunan tashin hankali dake addabar jihar.
A wani labarin kuma, anyi nasararkubutar da wasu yan mata guda 3 daga hannun barayin shanu a karamar hukumar Ningi dake jihar Bauchi. Jami'i mai hudda da jama'a na rundunar sojin kasa, kanar Sani Usman kakasheka ne ya bayyana hakan inda ya bayyana cewa mutane sun taimaka kwarai.
Asali: Legit.ng