Gasar cin kofin turai: Faransa da Switzerland sun tsallaka
Kasar Switzerland da kuma mai masaukin baki watau Faransa sun tsallake zagayen farko zuwa zagaye na biyu na gasar cin kofin kasashen turai bayan da suka buga kunnen doki babu wanda yaci wani a wasan su na karshe na yan rukunin 'A'.
Ko da yake dan wasan Faransa Paul Pogba ya kusa ya saka kollo a ragar abokan hammayar sa amma mai tsaron gidan kasar ta Switzerland Yann Sommer ya hana shi. Ita dai kasar ta Switzerland ta tsare gidan ta sosai inda ta hana Faransar zura mata kwallo ko da daya tare da hana ta lashe wasan na su na uku a jere.
A wani labarin kuma mai kama da wannan, Armando Sadiku na kasar Albania ya kafa tarihi a kasar tasu inda yaci kwallo daya tilon da kasar taci abokiyar karawar tata watau Kasar Romania inda wasan ya tashi 1-0. Akwai yiwuwar kasar ta Albania ta tsallaka zagaye na gaba idan ta samu nasarar zamewa cikin masu kwazo cikin wadan da suka gama na 3.
Yanzu dai bayan da yan rukunin 'A' suka kammala wasannin su, kasar Faransa ce ta daya da maki 7, Switzerland ta biyu da maki 5, sai Albania ta ukku da maki 3 sannan kuma Romania da maki 1 tal wacce kuma ta fita daga gasar.
Za dai a cigaba da gasar yau Litinin tsakanin kasar Rasha da Wales da kuma Slovakia da Ingla duk yan rukunin 'B'.
Asali: Legit.ng