Yarima gwarzon Shari’a ya aske Gemu

Yarima gwarzon Shari’a ya aske Gemu

- Tsohon gwamnan jihar Zamfara kuma Sanata a yanzu ya canza kamanni

- Ko kun tuna gwarzon shari’a wanda kuma ya shiga bakin duniya a sakamakon auren wata ‘yar shekara 13 ‘ya kasar Masar a ‘yan shekarun baya?

- Tsohon gwamnan jihar Zamfara Ahmed Yarima ya fita daga jerin Ustazai masu ajiye gemu.

Yarima gwarzon Shari’a ya aske Gemu
Yariman Bakura a Yanzu

Yeriman Bakura wanda ya yi suna da soma kaddamar da shari’ar Musulunci a jihar Zamfara a lokacin da ya ke gwamna, shi ne kuma wanda ya sake shiga kace-na-kace a sakamakon auren wata ‘yar Misira ‘yar shekara 13 a ‘yan shekarun bayan a lokacin yana Sanata.

Yanzu ma ya sake shiga wani kace-nacen a sakamakon aske gemu da sa kwat.

KU LURA: Za aka iya samun labara tsegunguma a manhajar Naij

An dai san Sanatan da kasancewa kullum a cikin shigar babbar riga da hula da kuma tumbujejen gemu da saje, amma a yanzu Sanatan ya canza shiga.

Kamar yadda aka ga tsohon gwamnan a Abuja a ‘yan kwanakin nan, gwarzon na shari’a ya koma shigar kwat da turoza da laktayin, ya kuma aske gemu da sajen da aka san cewa sunna ce, kuma alama ta dattijantaka a al’adar Hausawa.

Wannan sabuwar shiga ta Yariman Bakura ta janyo kace-nace musamman a dandalin sada zumunta da muhawara na intanet. Shin kuma ko menene ra’ayinku dangane da wannan birgiman hankakan?

 

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel