Labari da dumi-dumi: Tsagerun NDA sun fasa bututun mai
Tsagerun Neja Delta sun kara fasa bututun mai na kamfanin gwamnatin Najeriya NNPC dake cikin jihar Akwa Ibom.
A safiyar yau ne dai tsagerun suka sanar da ta'asar tasu ta fasa bututun mai dake a karamar hukumar Oruk Anam din jihar. Su dai tsagerun sun bayyana hakan ne ta shafin su na tuwita @NDAvengers.
Wata kungiyar tsagerun dai ta yankin ta bada sanarwar tsagaita wuta tare da yin na'am da tayin sasancin da gwamnatin tarayya tayi musu sannan kuma suka bayyana sharadin farko da gwamnati zata cika musu shine ta saki Sambo Dasuki tsohon mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro da dai sauransu.
Ranar 7 ga watan June ne dai shugaba Buhari ya bada umurnin a janye sojojin kasar daga yankin na tsawon sati 2 domin bada damar tattaunawa.
Asali: Legit.ng