Super Eagles: Kociya na so a mayar da shi na dun-dun-dun

Super Eagles: Kociya na so a mayar da shi na dun-dun-dun

-Kociya Salisu Yusuf na so a mayar da shi na dun-dun-dun

-Yusuf ya ce ba zai yarda ya zama mataimakin wani koci ba kuma

-Mai horas da ‘yan wasan ya jagorance ‘yan wasansa zuwa ga nasara a kan Mali da Luxenborg a watan ya wuce

Super Eagles: Kociya na so a mayar da shi na dun-dun-dun
Kociya Salisu Yusuf na Super Eagles

Mai horas da ‘yan wasan Super Eagles na wucin-gadi Salisu Yusuf ya ce zai iya zama cikakken mai horas da ‘yan wasan Super Eagles na Najeriya. Rahotanni daga wata majiya ta hukumar kula da kwallon kafa ta kasar na cewa, kociyan na rikon kwarya, zai koma karkashin wani kocin ne wanda za ta dauko daga kasar waje nan ba da dadewa ba. Domin a cewar majiyar, wasu ‘yan kasar Serbia su ukku na dakon mukamin.

Duk da wadannan rahotanni, Yusuf na da yakinin cewa ya yi rawar ganin da kasar ya kamata ta bashi wannan mukami na dun-dun-dun. Ba jeka-nayi-ka ba, domin a shekara daya da ta wuce Yusuf ya yi wa marigayi Stephen Keshi da Sunday Oliseh da kuma Samsom Siasia mataimaki, kafin ya jagoranci kulop din ga nasara a kan Mali da Luxemborg. A hirar su da shafin Africanfootball.com a intanet, Yusif dan shekara 53 ya ce: "Na gaji da zama mataimaki, domin zan iya wannan aiki bayan taimakawa Keshi da Oliseh da kuma Siasia.”

A wani labarin kuma, kyaftin din Super Eagles na riko, Ogenyi Onazi ya roki NFF da, ta kar da rushe masu kula da ‘yan wasan na yanzu, saboda su kai ga wakiltar kasar a gasar cin kofin duniya World Cup na 2018.        

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng