Abun al'ajabi: Sunan Allah ya fito a cikin kankana

Abun al'ajabi: Sunan Allah ya fito a cikin kankana

- Wani gida sun ga sunan Allah a cikin kankana

- Makwabta sai kawo musu ziyara suke domin ganin abun al 'ajabi

- Hakan ya faru ne a cikin wata mai alfarma watan Ramadana

A ranar alhamis ne Asif iqbal , mazanaunin Leicester a kasar ingila ya sayo kankana domin ya sha, yanka ta ke da wuya  sai ya ga wani abin al'ajabi, ya ga sunan Allah karara a cikin.

Abun al'ajabi: Sunan Allah ya fito a cikin kankana
Asif Iqbal kenan inda ya ga sunan Allah a cikin kankana

Asif da ganin haka, ya kira iyalen shi gaba daya su zo su shaida sunan Allah a cikin kankana. Jim da kadan, gidan su ta cika da yan kallo daga Makwabta da sauran mutane. Asif yace: “Mutane basu daina zuwa gani ba, har mun ba wasu yankan kankanan ma. Kai ba zan iya fada ma iyakan mutanen da suka zo ba saboda yawan su.

“Asif ya kara da cewa wannan rahama ce daga Allah , na tambayi malamai sun ce min daya daga cikin ayoyin Allah ne wanda ke nuna cewa akwai Allah musamman a cikin watan Ramadana.”

Wannan abun al'ajabin na kara haskaka hasken musulunci a wannan watan Ramadana, wata mai alfarma,  watan da musulmai a duk fadin duniya ke azumi biyayya ga umurnin da Ubangiji ya bayar a cikin Alkur'ani wanda aka saukar wa Manzon tsira Muhammad (tsira da amincin sa su tabbata a gare shi).

Abun al'ajabi: Sunan Allah ya fito a cikin kankana
sunan Allah cikin kankana

Wannan ba shi bane lokaci fari da sunan Allah ke fitowa a kan wasu halittu ba, a taba gani a cikin kifi, kwai, gero, harda jikin mutane kamar kai da kunne. Amma malaman musulunci sun ce wadannan ayoyin kawai alamu ne ba karaman wani ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel