Lalatattun hanyoyi na ba 'yan Legas wahala (Hotuna)

Lalatattun hanyoyi na ba 'yan Legas wahala (Hotuna)

-Mazauna titin Olufemi Ogunsola a karamar hukumar Ifako Ijaye na cikin tasku a sakamakon munanan hanyoyi

-Unguwar Olufemi Ogunsola ta kasance a cikin wannan hali na rashin kyan hanya shekaru aru-aru.

-Masu bin hanyar a kullum na kokawa da lalacewar hanyar da ta gaza tsawon mita 500.

Lalatattun hanyoyi na ba 'yan Legas wahala (Hotuna)
Akinwunmi Ambode

Ba fargabar saukar ruwan sama jama’ar Najeriya ke yi ba, sai dai fargabar lalacewar hanyoyi da suke dada kazancewa a lokaci na damuna sakamakon zaizayar kasa da ambaliya ruwa.

Legit.ng ta gano cewa da akwai wasu unguwanni a  Legas da ke fama a kullum da matsananciyar lalacewar hanyoyi.

KU KARANTA: An kama wani mutum akan cutar da wasu Yan mata

Wadansu daga cikin wadanda suke zaune a a irin wadannan wurare sun ce sun koka wa gwamnati ta hanyar aika wasiku ga Gwamna Ambode sakamakon kunnen uwar shegun da shugabannin kananan hukumominsu suka yi kan matsalar.

Daya daga cikin dalilan da mazauna titin Olufemi Ogunsola ya zama daban shi ne titin ya raba iyakar kananan hukumomin Ojudu da kuma Ijaye.

A lokacin  da Legit.ng  ta yi hira da wani mai sana’ar hayar babur wanda ya san halin da hanya ta ke ciki ya ce: “shugaban karamar hukumar Ifako Ijaye bai damu da ya gyara hanyar ba. Da akwai wasu hanyoyin da suka fi wannan lalacewa, wandanda ko ya kula. Ban kuma san dalilin da gwamna Ambode bai tsawatar masa ba, ko ma ya cire shi daga kan mukamin. Saboda rashin kyan hanyar ya shafi kowa”.

Wasu daga  hotunan lalacewar hanyar:

Lalatattun hanyoyi na ba 'yan Legas wahala (Hotuna)
Lalatattun hanyoyi na ba 'yan Legas wahala (Hotuna)
Lalatattun hanyoyi na ba 'yan Legas wahala (Hotuna)

Asali: Legit.ng

Online view pixel