Abin takaici : darajar Naira ta sake faduwa a kasuwan chanji
- Darajar Kudin najeriya ta sake faduwa a sabon tsarin chanji na talata yau a kasuwar chanji
- Kudin najeriyar da ta dunga sama da kasa a makkonin da suka gabata ta sake hawa
Game da wata masaniya a ma’aikatan chanji,an sayar da kudin najeriyan kimanin N355 akan dalan amurka 1 a ranar litinin, amma yau ta hau N360.
Masaniyar da ta nuna bacin ranta a bisa faduwan nairan ta ce “yan najeriya fa su shiryawa tsanani da kuncin rayuwa saboda rashin tsugunawan naira gad alar amurka a watanin da suka gabata.
Tunda gwamnatin tarayya taki fitowa ta yi shellar rage darajar kudin najeriyan, to ana mata kyakkyawan zaton cewa tana shiryawa yan Najeriya mafita daga cikin wannan al’amari ta hanyar rage darajar tendar najeriya da wuri domin ciwa birgewan IMF.
Ku karanta: Haddace Alkur'ani cikin sauki
“ A yanzu haka, baa bun da zan iya cewa face kudin najeriyan gaskiya ba ta da matsaya ga dala a kasuwan chanji saboda hauhawar ta yayi yawa a makonnin kusannan.
“ Idan ka shiga cikin kasuwa, zaka lura da cewan ‘yan chanjin ma basu da dalan amurka a hannun su saboda yayi tsada,ba’a samun shi. Shi ne dalilin da yasa darajar nairan ke ci gaba da faduwa. Gashi kuma kumburar tattalin arziki ta shigo, irin hawar da ba ta taba yin irin ta ba tun shekara 2010 , me kuma zamu ce?
“ Muna sa ran komai zai dawo dadai, dole ne mu yi kyakkyawan zato saboda shi kadai ne mafita yanzu a tunani na,” masaniyar mu ta fada mana.
Asali: Legit.ng