Kungiyar likitocin Nijeriya (NMA) zasu fara yajin aiki

Kungiyar likitocin Nijeriya (NMA) zasu fara yajin aiki

Kungiyar likitocin Nijeriya (NMA)Sun bada gargadin zasu fara yajin aiki na din-din ranar litinin 13 ga watan Juni.

-Shugaban likitocin Nijeriya(NMA)Dakta oladunni Adetola ya fada ma manema labarai a lokacin taronsu a garin Abeokuta babban birnin jihar agun lokacin da yake bayyana masu kan yanke shawarar da likitocin sukayi. A wata majiya munji cewa kungiyar likitocin tace in suka fara yajin Aikin na din-din zai kasance ranar litini da talata kawai ne ranar aiki har zuwa lokacin da gwamnatin ogun ta samar masu abinda suka bukata.

Daga cikin abubuwan da likitocin suka bukata ya kunshi`Karin likitoci,samar da magunguna adakin shan magani,samar da ingantattun dakin gwaje-gwaje da inganta ayyuka.  Shugaban likitocin yace. “A ce likita daya yake aiki a babban asibiti ai wannan abin takaici ne,yawancin yawancin asibitocin mu basu da rabin ma'aikatan da suke da shi shekara bakwai zuwa takwas da suka wuce.

"Dakunan gwaje gwajen basu da ingantattun kayan aiki,haka kuma dakin magungunan mu babu magunguna,wanda ya tilasta al'ummamu fita dole da samun magunguna ingantattu. Lokacin da manema labarai suka tambayi shugaban in sun taba kai korafinsu a kan bukatun sun ga gwamnatin da kuma tura korafinsu hanyoyin da suka da ce“shugaban ya amsa masu da cewa sun rubuta dinbin wasiku zuwa in da ya dace dan gyarawa. A kungiyance ya kamata muyi a dalci ka yarde mana da al'umma suka yi.Lafiya hakki ce akan duk wani dan kasa,kuma duk wani dan jahar ogun ya cancanci ingantaccen kiwon lafiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng