Marigayi Shuaibu Amodu na bin NFF albashin watanni 2

Marigayi Shuaibu Amodu na bin NFF albashin watanni 2

- Humkumar kula da kwallon kafa ta Najeriya amsa cewa marigayi kociya Shua’ibu Amodu nabin ta albashin watanni biyu.

- Za’a biya iyalan mamacin albashin da ya ke bi

- Amodu ya rasu a ranar Asabar 11 ga watan Yuni bayan ya koka ciwon kirji

Hukumar kula da kwallon kafa ta Najeriya (NFF)ta ce marigayi tsohon kocin Super Eagles Shu’aibu Amodu na bin ta albashin watanni biyu. A wani sakon ta dandalin sada zumunta da muhawara na Twitter a intanet, hukumar ta bayyana cewa za ta biya iyalansa albashin da yak e bi.

Babban sakataren hukumar Mohammed Sanusi  ya ce mabobin da hukumar na bin ta albashin watanni biyu. An sanar mutuwar  tsohon  mai horas da ‘yan wasan Super Eagles din ne har sau hudu  a safiyar ranar Asabar 11 ga watan Yuni 2016

Ya mutu ne a daren  Juma’a jim kadan bayan ya koka da jin wani zafi a kirjinsa  a wani sako da NFF ta aika Twitter. Rahotanni na cewa ya mutu ne a sakamakon wata rashin lafiya da ba’a bayyana ba, yain da kuma aka kai gawarsa dakin ajiye gawa da aka sa wa sunan Stella Obasanjo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng