Tsagerun Nija Delta sun kara fasa bututun mai na Agip

Tsagerun Nija Delta sun kara fasa bututun mai na Agip

Tsagerun nan masu fada da gwamnati a yankin Naija delta sun ce sun fasa wani bututun mai na Agip dake garin Obi Obi Brass. A wata sananr wa da tsagerun suka fitar ta shafin su na tuwita sunce bututun da suka fasa yana a yankin jihar Bayelsa ne.

Tsagerun Nija Delta sun kara fasa bututun mai na Agip
Tsagerun Nija Delta Avengers

Mai karatu zai iya tunawa cewar tsagerun dai sun bijirema tayin sasanci da gwamnatin tarayya tayi masu duk kuwa da cewa gwamnatin ta janye dukkan dakarun ta daga yankin mai arzikin mai.

A hannu daya kuma tsagerun sun bayyana jin dadin su dangane da kasashen waje da suka bar sayen danyen mai daga Najeriya. Su dai tsagerun sun sha alwashin hana kasar nan anfani da albarkatun man fetur din ta dake a yankin su.

KU KARANTA:  Zamu kai hari akan Gwamnonin Nija Delta - Yan Bindiga

Wannan na zuwa ne bayan da kungiyar tsagerun ta kai hare-hare akan bututu daban-daban na mai inda hakan ya jaza asara mai girma ga jama'a da kuma gwamnatin Najeriya. Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa zata tsagaita wuta inda take cigaba da kokarin samadda da yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin ta da kungiyar.

A wani labarin kuma, shugaban majalisar Dattawa, Sanata Bukola Saraki ya bayyana cewa ya halarci sallar juma'a a babban masallacin Abuja inda sukayi addu'a ga Allah daya bawa shugaban kasa Muhammadu Buhari lafiya kuma ya taimake shi.

Shugaban majalisar ya bayyana wannan ne a shafin shi na Twitter inda yake bayyana cewa zasu cigaba da ba shugaban kasa Muhammadu Buhari dukkanin goyon bayan da yake bukata domin kawo canji a tarayyar Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng