Kebbi ta zo ta 2 a kiwo, za kuma ta hada hannu da Lagos

Kebbi ta zo ta 2 a kiwo, za kuma ta hada hannu da Lagos

- Jihar kebbi ita ce ta biyu a kiwon dabbobi a kididdigar da Ma’aikatar ayyukan gona ta yi a Najeriya

- Gwamnan jihar Kebbi Abubakar Bagudu ya ce yawan Alkaman da jihar ta noma ya karu da kashi 300, ana kuma sa rai zai dada karuwa zuwa kashi 1000 kafin watan Oktoba

Kebbi ta zo ta 2 a kiwo, za kuma ta hada hannu da Lagos
Gwamnan Jihar Kebbi

Jihar Kebbi ta kasance ta biyu a yawan kiwo dabbobi, a kididddigar da Ma’aikatar ayyukan gona ta Najeriya ta yi. A yayin da ya ke jawabi a Birnin-Kebbi a yayin bikin sanya hannu a wata yarjejeniya da aka kulla tsakanin gwamnatin jihar da ta jihar Lagos, Abubakar Bagudu ya ce jiharsa na bin bayan jihar Yobe a kiwo dabbbobi wacce kuma ta ke fitar da su zuwa sauran jihohin Najeriya.

Bagudu ya kara da cewa sauran abubuwan da jihar ke fitarwa sun hada da busasshen kifi daga kananan hukumomin Argungu da Yawuri, da man gyada daga karamar hukumar Mayahama da kuma noman Ridi da Dawa da kuma sauran nau’in abinci masu daban-daban.

Ya kuma ce noman Alkama a jihar ya karu da kashi 300 ,ana kuma sa ran zai sake karuwa zuwa kashi 1000 kafin watan Oktoba. Wannan sa rai, in ji gwamnan, sakamakon gagarumin tallafin da manoma suka samu ne daga gwamnatin tarayya ta hannun Babban bankin kasar. “Gasa mu ke yi da kasashen da Nigeria ke shigo da kayyakin”, a cewar Bagudu.

Bagudu ya kuma kara da cewa ziyarar da takwaransa na jihar Lagos Akinwumin Ambode ya kawo masa, wani mataki ne na karfafa dagantakar ayyukan noma a tsakanin jihohin biyu. Sannan ya ci gaba da cewa kawancen da suka kulla zai sa dan ban a habaka tattalin arzikin jihohin da kuma Najeriya baki daya.

A nasa jawabin, gwammna jihar Legas ya ce yarjejeniyar da su ka kulla ta fannni ayyukan gona da jihar Kebbi, ta zo daidai da manufofin gwamnatin tarayya na baza hannu a tattalin arzikin kasar wanda hakan zai samar da aikin yi ga ‘yan kasar.

Ambode ya ci gaba da cewa ziyarar, wata manuniya ce ta kudurinsa na karfafa dangon zumunci a tsakanin jihohin kasar wanda hakan zai kara habbaka tattalin arzikin jama’ar kasar ne.

“Wannan kawance an kulla shi ne don gaba, kuma manuniya ce ga cewa jihohin biyu sun amince da su taimakawa shirye-shiryen shugaba Muhammadu Buhari” in ji Ambode.

Gwamnan jihar Legas din ya kai ziyara a masana’antar casar shinkafa ta Labana, sannan ya kalli wani dan kwarya-kwarya bikin nunin amfanin gona a Birnin-Kebbi, ya kuma kai ziyarar ban girma ga sarkin Gwandu da sarkin Argungu.

Idan za’a iya tunawa yarjejeniyar da jihohin biyu suka kulla a watan Maris, ya mayar da hankali ne kan bunkasa noman Shinkafa da Alkama da Gyada da Masara da Gero, da Rake da kuma samar da Shanu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng