Manyan mutane ne suka halarci gasar wasan Polo a Kaduna

Manyan mutane ne suka halarci gasar wasan Polo a Kaduna

A gasar wasan dawakai na wannan Shekara an zo da zababbun dawakai daga Argentina. Gasar wacce aka yiwa lakabi da kasar karni, an shirya ta ne domin murnar cika kasar Argentina Shekaru 200 da samun 'yancin kai.

Manyan mutane ne suka halarci gasar wasan Polo a Kaduna

Bikin gasar ya samu halartar ya samu halaryar manyan mutane cikin har da jakadan Argentina a Najeriya Ambasada Gustavo Dzugala.

KU KARANTA: Niger Delta Avengers sun sha alwashin gano masu laifi

A bikin bude gasar mai kayatarwa ya samu halartar Barbara Zingg wata fitacciyar 'yar wasan Polo wacce ta yi hawa rike da tutar Argentina. Sauran many an baki a wurin sun hada a jakadun kashen Ecuador da Britaniya da Poland da Denmark da kuma wasu jami'ai daga wasu ofisoshin jakadancin kasashen waje da ke Najeriya. Shi ma Mai martaba sarkin Zazzau ya aika da wakilinsa zuwa bikin.

A wani babban labari kuma, kungiyar wasan Polo SA Poloafrica ta bayyana farin cikinta da shiga gasar Polon na fifth chukka da wani wasan a wurin shakatawa na Country Club a Kaduna.

'Yan wasan dawakan na Afrika ta kudu sum hada da Modaku Lepathi da Moefa Ralebenya da Thabo Mofokeng da Thapelo Mothijoa da kuma Montoeli Ntoeleng wandanda da dukkanninsu bakaken fata ne marasa galihu daga unguwanni yaku-bayi na Afrika ta kudu, kuma su ne kadai wadanda ba 'yan Najeriya ba a tawagar mutane 15 na 'yan wasan cin kofin na UNICEF, Wanda aka bude bukukuwan da bikin na mako guda da wasan na wannan shekarar.

'Yan wasan polon na garin Mandela sun koma kasar su hannu na dukan cinya, bayan Gaza samun nasara a wasanni 4 Wanda zai kai su ga karshe, sai dai ba za su manta d zamansa a Najeriya ba na kwanaki Biyar ganin yadda suka rika santin wurin shakatawa na filin wasan kwallon polo na fifth chukka.

"Mun ji dadin zaman mu a wannan wurin shakatawa Wanda kuma ya nuna cewa mutanen Nigeria mutanen kirki ne haba-haba da baki. A yanzu haka muna sa ran sake dawowa Shekarau mai zuwa". A cewar kyafyom din 'yan wasan Mathojoa, Dan Shekarau 23, na kungiyar SA Poloafrica.

Daya daga cikin 'yan wasan Ntoeleng Wanda ya jagoranci nasarar da ta suka samu akan Newline Farms da kuma Aerovote yayi amanna da cewa wasunsu a Najeriya zai sa su kara kwarewa a wasan na Polo.

Dan Shekarau 21 da haihuwa ya kara da cewa: " irin wannan mu'amilla na da kyau saboda yadda ake wasan a Najeriya ya banbanta da yadda mu ke yi a Africa ta kudu."

"A nan dai ka yi sukuwa sosai sannan ka daki kwallon, Wanda hakan ya burge masu kallo, idan muka koma gida za kara da wannan salo ga irin namu salon. Kuma babu shakka hakan zai taimaka matuka."

Asali: Legit.ng

Online view pixel