An Gano Wasu Kaddarorin Tsohon Shugaban Kastam

An Gano Wasu Kaddarorin Tsohon Shugaban Kastam

Kamar yadda majiyar mu ta Sahara Reporters ta ruwaito, tsohon shugaban hukumar shige-da-fice ta kasa watau kostan Abdullahi Inde Dikko ya yadda da tuhumar da akeyi masa ta mallakar kadarorin da suka kai darajar dalar amurka millian hamsin ($50m) a Dubai.

An Gano Wasu Kaddarorin Tsohon Shugaban Kastam
Tsohon shugaban kasar Nijeriya, Dakta Goodluck Jonathan

Tun farko dai Dikko Inde din ya bayyana da kansa cewar yana da gida a Abuja da kuma babbar gona a garin sa dake a Jihar Katsina.

In za'a iya tunawa da a cikin watan Janairu na wannan shekarar ne hukumar hana cin hanci da rashawa ta kasa watau EFCC ta ziyarci gidan na Dikko Inde dake a Abuja.

KU KARANTA: Ba za'a binciki kudaden kamfe din mu ba - APC

Wasu majiyoyi da ke kusa da tsohon shugaban sun kuma bayyana cewar shi Alhaji Dikko Inden yanzu haka yana fama ne da cutar ciwon daji watau prostate Cancer.

A cewar wani makusancin nasa ya bayyana cewar ba'a kama tsohon jami'in bane har yanzu don gudun kar ya rasu a tsare wanda kuma hakan zai kara bada wahala wajen kwato dukiyar tasa.

Abdullahi Dikko Inde dai ya rike kujerar shugaban hukumar kwastan din ta Najeria ne daga watan Agusta na shekarar 2009 zuwa Agusta na 2015. A lokacin shi kuma an samu cigaba da sauye-sauye da dama a hukumar.

A wani labarin kuma, tsohon shugaban kasa Jonathan ya  dawo daga tafiyar da yayi a kasar waje inda a halin yanzu yana garin su na Otuoke inda gidan su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng