Dalilin da yasa muka kashe magoya bayan Biyafara - Soji
Kanun labaru na jaridun yau 1 ga Yuli sun ta’allaka ne a kan karon da akayi tsakanin magoya bayan masu son Biyafara da hukumomin soja na Nijeriya.
Legit.ng ta ruhoto maku cewa yayin da ake bikin juyowar ranar Biyafara na marigayi Dim Chukuemeka Odumegu Ojuku, al’amarin ya kazamce yau Litinin yayin da ‘yan sanda suka tarwatsa masu zanga-zangar da barkonon tsofuwa wanda ya jaza turmutsutsi ya kuma kawo asarar rayuka harda kuma kame wasu ‘ya’yan kungiyar.
KU KARANTA: Tsagerun Nija Delta sun sha alwashin hallaka Buhari
Amma rohota daga jaridar Vanguard na cewa hukumar sojoji na bayanin cewa suna aiki da dokokin soja na kare kawunansu tare kuma gadar Niger mai mahimmanci.
Jawabi daga bakin mukaddashin kakakin hukumar sojoji Kanar H.A Gambo na cewa sun dauki matakan ne domin hana masu zanga-zangar samun tallafi daga wasu mutane masu dannowa daga bangaren Onitsha ta wajen gadar Niger.
Idan za'a iya tunawa, a makon daya wuce sojojin Najeriya suka kama wasu daga cikin manyan tsagerun na Nija Delta. Wannan yazo ne bayan da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba sojojin Najeriya umurni dasu murkushe kungiyar tsagerun. Sojojin har sun fara kai jami'an su da kuma kayan yaki inda suke shirin murkushe kungiyar.
A wani labarin kuma, shugaban kasa Muhammadu Buhari zaya ziyarci Nija Delta inda zaya kaddamar da gyaran kasar Ogoni dake cikin jihar Rivers. Fasa bututun mai ya lalata kasar inda yake kashe kifaye da sauran halittun ruwa. Dama a lokacin yakin neman shugaban kasa, shugaba Buhari ya sha alwashin gyara kasar.
Shekarar shugaban kasa Muhammadu Buhari 1 ke nan akan mulki. Gwamnatin nashi na fuskantar kalubale daga raguwar farashin Mai a kasuwannin duniya, sannan kuma fannin mulki da fannin shari'a da yan majalisa na fuskantar rashin jituwa inda ake cigaba da samun takin sa'a a cikin gwamnatin ta shugaba Muhmmadu Buhari.
Asali: Legit.ng