Naira ta kare N285 akan Dala Daya a Yau
- Matsalar Naira na cigaba da addabar Najeriya
- Dala Daya ta koma Naira 285 a bankuna a cigaba da wahalar da ake fuskanta
Duk da cewa babban bankin Najeriya bai fiddo da cikakkun bayanan canjin kudi ba izuwa yanzu ba, neman canjin kudaden na cigaba da karuwa kuma Dala 1 ta koma Naira 285. Jaridar Guardian ta ruwaito labarin.
Takunkumin da gwamnati ta sanya ma masu canjin kudade duk da cewa mutane zasu iya zuwa Bankuna nema canjin kudin.Bayan da wannan canjin tsarin ya samu, wannan ne ya sanya Bankuna suka suka canja farashin canji inda ya canza daga yadda yake zuwa 285.
Sabon tsarin zaya ba Bankuna da yan canji damar suje su nemo Dala da kansu su ringa saida ta a farshin kasuwa ba tare da sa hannun bwamnati a ciki ba. Ada, farashin canjin daga 197 zuwa 199, amma bayan da aka bayyana sabon tsarin sai ya koma N285.
An samu Karin kudi har na kasha 43 daga yadda yake ada na 199. Wani mai sharhi ya bayyana cewa ya bayyana cewa kasuwar tana canza kanta ne a yadda lamurra ke kasancewa.
Amma a shafin yanar gizo na Babban bankin Najeriya ya bayyana cewa farashin canjin na Dala Daya yana nan akan 197.
Amma shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da a shigo da sabon tsarin canjin kudin wanda hakan zaya bada dama kudin canjin ya ringa canza a yayin da kasuwar ta canza.
A bangare daya kuma, Malam Garba Shehu ya bayyana a wata fira da NTA cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana ba sau daya ba s au biyu ba cewa baza ya yadda a rage darajar Naira ba. A karshen makon nan daya wuce, shugaban kasa Buhari ya bayyana cewa zaya sanya ido akan yadda ake samun canjin kudin.
A wani labarin kuma, tsohon shugaban kasa Atiku Abubakar da shugaban jam’iyyar APC Cif John Oyegun sun shirya tsohon Gwamnan Jihar Legas, Bola Tinubu da shugaban majalisar Dattawa, Abubakar Bukola Saraki.
Asali: Legit.ng