Manyan labarai guda 10 wadanda sukayi fice ran Litinin

Manyan labarai guda 10 wadanda sukayi fice ran Litinin

Legit.ng ta tattara maku manyan labaran da sukayi fice a ranar Litinin 30 ga watan Mayu. ku duba domim ku samu wadannan manyan labaran.

Manyan labarai guda 10 wadanda sukayi fice ran Litinin

1. Sojoji sun kashe mutane 30 masu rajin Biafra

A inda mutane suka taro domin murnar Ojukwu, sojojin Najeriya sun bude ma mutanen wuta inda suka kashe akalla 30.

2. An gano wanda ke bayan tsagerun Niger Delta Avengers 

Wani tsohon tsageran Niger Delta ya bayyana cewa babu wasu tsageru dake akwai a Nija Delta a yanzu, wani ne ya kafa kungiyar.

3. Sojojin Najeriya sun bude ma Yan sandan Najeriya wuta a Bauchi

Sojojin Najeriya sun bude ma yan sandan Najeriya wuta a Bauchi inda suka halbe motar su a yayin da suke a wani Check point.

4. Sojojin Najeriya sun shiga kauyen su Tompolo sun yi ma mutane barazana

Sojojin Najeriya sun shiga kauyen daya daga cikin manyan tsofaffin tsagerun Nija Delta inda suka yi ma mutanen kauyen nasu barazana.

5. Yara masu fama da lalurori

Legit.ng daga cikin manyan rahotannin ta ta ruwaito yadda yara masu lalurori suka fama da rayuwa.

6. Yadda Buhari ya canza Najeriya

Editan Legit.ng na turanci ya bayyana yadda shugaban kasar najeriya ya canza Najeriya a cikin shekarar shi guda yana mulki

7. Manyan jawaban shugaban kasa Buhari na amsar rantsuwa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa "Ni na kowa ne, ni bana kowa bane"

8. Karuwa ta yanke ma wani mutum gaba a Kenya

Bayan da suka gama masha'a sai yaki biyan ta kudin ta, sai ta yanke mashi gaba.

9. An ga fastar Shettima da Okorocha

Rade-radi na nuna cewa Gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima na shirin tsayawa takara a 2019 inda Gwamnan Jihar Imo, Rochas, zaya yi mashi mataimaki.

10. Nayi mamaki yadda Jonathan ya yadda na kada shi - Buhari

Shugaba Buhari a jiya ya bayyana cewa yayi mamaki yadda tsohon shugaban kasa Jonathan ya yadda shi Buhari ya kasa shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng