Manyan labarai guda 10 wadanda sukayi fice a ranar Laraba

Manyan labarai guda 10 wadanda sukayi fice a ranar Laraba

Legit.ng tattara maku manyan labarai guda 10 wadanda sukayi fice a ranar Laraba 25 ga watan Mayu na 2016. Ku duba domin ku samu wadannan manyan labaran.

Manyan labarai guda 10 wadanda sukayi fice a ranar Laraba
Sanata Bukol Saraki a kotun CCT

1. Sanata Bukola Saraki ya koma kotun CCT

Shugaban majalisar Dattawan Najeriya, Bukola Saraki ya sake komawa kotun CCT a cigaba da shari'ar shi da ake gudanarwa.

2. Boko Haram ta kara kai hari akan garuruwa 5 a jihar Borno

Boko Haram ta kai hari akan kyayuka 5 wadanda suke kusa da Ladin Buta kusa da Khaddamari dake a karamar hukumar Jere a jihar Borno.

3. An kama wasu da ake zargin cewa su suka kai hari a Nimbo

An kama wasu mutane da ake zargin cewa su suka kai hari a garin Nimbo dake a karamar hukumar Uzo-Uwanni a jihar Enugu.

4. Tsohon gwamnan Kaduna ya mutu

A jiya ne Manjo Janar Abubakar Tanko Ayuba ya rasu da shekaru 70. An taba bashi Kambi Nelson Mandela na kakkyawan shugabanci.

5. Gwamnatin tayi nadin shugabannin wasu manyan hukumomi

A jiya ne Gwamnatin Najeriya ta nada sabbin shugabanin manyan hukumomin dake karkashin ma'aikatar labarai. Hukumomin sune NTA, da sauran su.

6. Gwamnatin Tarayya ta bada hutu a ranar ga watan Mayu

Gwamnatin Najeriya ta bada hutu a ranar 30 ga watan Mayu domin a gudanar da hutun ranar Damakaradiyya.

7. An kama wata mata na kokarin yima wani Fasto Sherri

Wata mata yar shekara 30 mai suna Joy Ogundare zata gurfana a gaban Babbar Kotun Kano akan kokarin yima ani Fasto Sherri.

8. Allah wadarai da karin farashin Mai - Fayose

Gwamnan jihar Ekiti yayi Allah wadai da karin farashin Mai a karkashin Gwamnatin Buhari

9. An kama wasu yan Najeriya masu karuwanci a kasar Rasha

Wasu Yan Mata da ake zargin cewa karuwai an kama su a klasar Rasha inda aka tozarta su.

10. An ga gawar Sanata Ofia Nwali

Bayan da aka tsinci gawar shi a cikin Rijiya, jami'an Yn sanda sun bayyana cewa suna gudanar da biki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel