Buhari ya nada Ja'afar matsayin shugaban jam'ian gidan Yari

Buhari ya nada Ja'afar matsayin shugaban jam'ian gidan Yari

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Mista Ahmed Ja'afaru a matsayin shugaban jami'an gidan Yari

- Ahmed ya jima yana aiki a hukumar jami'an gidan yari 

- Shi mataimakin shugaban gidan Yari ne a babbar Hedikwatar a Abuja

Buhari ya nada Ja'afar matsayin shugaban jam'ian gidan Yari
Ofishin Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari a fadar shugaban kasa dake Abuja

Rahotanni daga Kamfanin Dillacin Labaran Najeriya (NAN), na nuna cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin Mista Ahmed Ja'afaru a matsayin sabon shugaban jami'an hukumar gidan Yari. Babban Sakataren hukumar cikin gida, Bassey Akpanyung ne ya bayyana hakan inda yake tabbatar da hakan.

Nadin nashi yazo bayan da ya jima yana aiki a hukumar inda ya kai matsayin mataimakin shugaban hukumar kuma yake aiki a Hedikwatar hukumar a babban birnin Tarayar Najeriya, Abuja.

Kamfanin Dillacin labaran Najeriya ya bayyana cewa Ahmed zaya karbi jagorancin hukumar ne daga tsohon shugaban hukumar, Dakta Peter Ekpendu wanda wa'adin aikin shi ya zo karshe a yau, Talata 24 ga watan Mayu na 2016.

Takardar aikin ta bayyana cewa a yau za'a karbi ragamar hukumar kiuma ya cigaba da aikin a matsayin sabon shugaban hukumar.

Idan za'a iya tunawa, a makon daya wuce ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da dakatar da shugaban hukumar shige da fice ta Najeriya daga aiki. Wannan yazo ne bayan da wasu korafe korafe da aka aika ma shugaban kasan a game da shi inda hakan ya sanya aka dauki matakin akan shi.

A wani labarin kuma, Sifeton Yan sanda, Solomon Arase ya bayyana cewa wasu shugabannin jam'iyyar PDP na shirin tada hankalin jama'a ta hanyar shigowa da wasu yan daba domin suyi zanga-zanga sannan kuma su amshe Hedikwatar jam'iiayr inda zasu zauna a cikin Ofishin ta dake a wadata Plaza. Shugaban yan sandan ya gargade su da aikata hakan inda ya bayyana cewa duk wanda ya karya doka zaya fuskanci hushin hukuma

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng