An kama mutanen da suka kashe Janar Mamman Shuwa

An kama mutanen da suka kashe Janar Mamman Shuwa

An kama wadansu mutane wadanda ake zargin su suka kashe Janar Mammam Shuwa.

An kama mutanen da suka kashe Janar Mamman Shuwa

KU KARANTA: Manyan labarai wadanda sukayi fice a ranar Litinin

Janar Mamman shuwa dai shine Kwamanda na farko na Dibishan ta 1, kuma shi ya samu yabo sosai bayan da aka gama yakin basasa. Yan Bindiga ne suka halbe shi a shekarar 2012.

Hukumar soji ta tabbatar da cewa ta kama wasu mutane wadanda suke zargin cewa su suka kashe gwarzon jarumin.

A cewar mukaddashin jami'i mai hudda da jama'a na sojin kasa, Kanar Kakasheka Usman, sashen tattara bayanai na soji ya biyo mutanen 2 daga Maiduguri zuwa Kano a inda nan ne aka kama su.

A inda ake nuna masu laifin, Kwamandan Birigid din ta Kano, Birigediya Hamisu Hassan, ya bayyana cewa an kama sune bayan da aka samu bayanai masu tsawo sosai.

Yan ta'addan na Boko Haram an kama sune a Unguwar Hotoro dake a garin Kano, a cewar jaridar The Nation.

Janar hassan ya bayyana cewa Ali Muhammad, wanda aka fi sani da Amir, dan shekara 25,  Malamin kungiyar ne a garin Baga. yayi tafiyayya daga Baga zuwa Maiduguri a shekarar 2009 domin ya karfafa Muhammad Yusuf a lokacin da yake fada a jami'an tsaro.

An bayyana cewa shi na kusa ne sosai ga wanda ya kashe Janar Mamman Shuwa.

A cewar kwamandan. an kama yan ta'addan ne guda 2 a ranar 30 ga watan Afrillu, da kuma a ranar 1 ga watan mayu.

Binciken da aka fara gudanarwa ya nuna cewa, Muhammad Sani Nafiu dan shekara 35 ne ya taimaki dan ta'addan daya halbe Janar Mamman Shuwa.

Daga cikin abubuwan da aka amshe daga hannun Ali Muhammad sun hada da Mota kirar Volkswagen, Gulf, mai lamba, 775 PP, an kama Wayar Salula daga hannun shi da kuma kudi tsabar Naira 20,100.

Janar Hassan yace " Ina kara tabbatar masu da matsayar mu akan abunda Hafsin Sojin Kasa, Tukur Yusuf Buratai, wajen tabbatar da cewa mun kori yan Boko Haram daga iyakar Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng